Hanyoyin hana daukar ciki na mata - Android Pols

Hanyoyin hana daukar ciki na mata
Hanyoyin hana daukar ciki


Matan da ke shan maganin hana daukar ciki idan suna shan taba, sun fi fuskantar kamuwa da ciwon gudajin jini da ke hana jinin gudana a jijiyoyi (thrombosis), da kuma ciwon zuciya.


Maganin da za a sha: kwayar hana daukar ciki mai kunshe da sinadaran da ke hana kwayayen nan biyu (ovaries) sakin kwai daya a kowane wata.

Yadda za a sha: yawancin lokuta ana shan kwayoyin har tsawon kwana ashirin da daya, sannan a daina sha har kwana bakwai. Macce na iya barin shan kwayoyin a duk lokacin da ta ke so, idan tana son ta yi ciki.


Amfanin kwayoyin hana daukar ciki

Kwayoyin hana daukar ciki suna da saukin amfani, watakila su rage zafın al'ada, mai yiwuwa kuma su hana kamuwa da wani nau'i na kansar mahaifa ko farji.


Illolin Magungunan Hana Daukar Ciki

Dole ne a sha maganin a kullum, kuma ba sa hana kamuwa da cututukan da ake dauka ta hanyar jima'i ko kuma kwayar cutar HIV; matan da ke shan maganin hana daukar ciki idan suna kuma shan taba, sun fi fuskantar kamuwa da ciwon gudajin jini da ke hana jinin gudana a jijiyoyi (thrombosis), da kuma ciwon zuciya.


Allurar hana daukar ciki 

Kamar dai maganin hana daukar ciki, irin wadannan alluran na dauke da wani sinadari da ke hana ciki shiga.

Yadda ake daukar allurar: kowane wata uku, ko wata biyu, ko kuma kowane wata don hana saukar kwai (ovulation).

Amfanin allurar hana daukar ciki: da zarar an yi allurar, ba wani matakin da za a dauka har lokacin da za a sake yin wata.

Cikas din allurar hana haihuwa: dole sai an je asibiti; tana iya sa al'ada ta dauke ko kuma a rika yin ta ba a kai a kai ba; bata hana kamuwa da cututukan da ake dauka ta hanyar tarawa ko kuma kwayar cutar HIV.

Kwaroron roba na mata: wata 'yar jaka ta roba, wadda ba matsatsiya ba, wadda bakinta ke kewaye dukan bakin farji idan an saka. 

Amfaninta shine, tana yin kariya daga wasu cututukan da ake dauka ta hanyar tarawa, da kuma kwayar cutar HIV. Rashin amfaninta: tana iya jawo cikas idan ana tarawa; dole sai an san yadda za a yi amfani da ita.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post