Halayyar Matan Social Media

Halayyar Matan Social Media 


Irin halayyar matan social media da Samari za su kula da halayensu 


Yamnata suna complain akan samarinsu basa kulawa dasu to su samari ai ba mahaukata bane, In kaji mace tace saurayinta yana kulawa da ita nufin ta fa saurayin da zai sa ta a gaba yayi ta kashe mata kudade yana mata dawainiya kamar bai san zafin kudaden ba ko kuma ba wahala yake yi ya samu ba. 


Mace idan kace mata kwana biyu bana ganinki online sai kayi sa'a ne ma zata ce maka data ne matsalanta wata sai kaga tana neman daura maka nauyin siya mata waya. 


Wata zaka ce mata tachi abinchi kuwa kawai sai ta fara maganar ka siya mata kaza ko shawarma wata zatayi status kamar tana cikin damuwa kana mata reply zata fara maka maganar bata da kudi. 


Gaba daya in kasan baka da kudi to kar ma ka fara cewa zaka wani bawa mace kulawa wallahi ko kiranta ka fiyeyi don kaji yadda take kafin ta daga wata sai ta fara zaginka tace wannan ya cika takura. 


Kulawa a wajen wasu matan ka tanaji kudi kawai daga sun dan yi motsi ko yaya ne ka jikasu da kudi amma duk wani kiran wayarka da wani zuwa zanchenka da wani yi mata text duk na banza ne. Da fatan Samari za'a kula


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post