Alamomin Daukewar Jinin Haila |
Alamomin Yadda Mace Za Ta Gane Daukewar Jinin Haila
Mun shirya kawo muku wannan darasi na yau kan alamomin da mata musamman matasa wanda suka fara balaga yadda zasu gane daukewar jinin al'ada da kuma abubuwan da ya kamata su yi.
Idan jinin haila ya dauke akwai alama da shara'a ta sanya domin ya zama shine manuniya ko alamu akan cewar al'adarki ta dauke har sai kuma wani lokacin.
Alamomin Daukewar Jinin Haila
Wadannan alamu sun kasu gida biyu kuma kowacce tana cin gashin kantane, sune kamar haka:
1. Bushewar Farji: Abinda ake nufi anan shine mace ta shigar da kyalle ko auduga cikin gabanta ta fito da ita busasshiya bawani jini a tare da ita, to da zarar taga haka to ta tabbata al'adarta ta dauke.
2. Fitar Farin Kumfa: wannan wani ruwane fari mai laushi da yake zuwa a karshan al'ada, idan mace ta ga irin haka a karshan al'adarta to ta sani ta kammala.
Wadannan alamomi sune suke nuna daukewar al'adar mace, idan mace bata taba ganin al'adaba sai a wannan karon sai ta fara ganin bushewar gaba to kai tsaye ta samu tsarki ba sai ta jira fitar farar kumfa ba. Amma idan wacce ta saba gani ne sai taga bushewar gaba to malamai sukace zata dan saurara kadan domin jiran farin kumfa, amma jinkirin bazai kai ga fitar zababban lokacin sallah ba.
A takaice dai kowanne daya daga cikin wadannan alamomin daukewar al'ada da muka bayyana yana nuna samuwar tsarki ba lalle sai sun hadu a lokaci gudaba, da zarar alamar ganin tsarki ta tabbata sai tayi wankan tsarki domin taci gaba da ibada.
Domin idan batayi wankaba koda jinin ya dauke mijinta bazai sadu da itaba ba kuma ba zata yi sallaba, da dai sauransu. Idan mace taga ruwa mai fatsi-fatsi ko diddiga-diddiga bayan daukewar jinin Haila to kada ta damu taci gaba da harkokinta na ibada, dama matsalar idan ta ganshi a farkon jinine, amma idan a karshen jinine to wannan ba komai.
Mace ta dinga duba samun tsarkinta a lokacin da zata kwanta bacci da kuma lokacin sallar asuba, amma ba'ace ta tashi cikin dareba domin ta duba. Idan mai al'ada ko mai biki (jinin haihuwa) taga tsarki kafın rana ta fadi to sallar azahar da la'asar sun hau kanta.
Hakanan kuma idan taga tsarki kafın hudowar alfijir shima wanka ya hau kanta. Wannan dai sune manyan alamomin daukewar jinin haila ga mace da za tai saurin ganewa. Munyi wannan bayani ne musamman domin Matasan mata da basu san alamomi da kuma daukewar jinin al'ada ba.