Dalilin Da Yasa Mata Sukafi Jarabar Jin Sha'awa A Lokacin Sanyi |
A lokacin sanyi mata suna son samun dumi a jikinsu, wannan yasa idan suna da aure suke makalkalewa mazajensu
A dabi'ance, mata sunfi maza jaraba a lokacin yanayin sanyi. Su kuma maza a lokacin zafi.
Sai dai ana iya samun sauyi game da hakan ga wasu mutanen. Amma kamar yadda bincike ya tabbar su mata jarabansu na son jima'i yana karuwa ne da kashi 15 a lokacin da ake sanyi.
Sai dai kuma bincike ya tabbatar da cewa, 'ya'yan marainan maza yafi tara maniyi a lokacin sanyi shi yasa aka fi samun daukan ciki a watannin sanyi fiye da lokacin zafi.
A lokacin sanyi mata suna son samun dumi a jikinsu, wannan yasa idan suna da aure suke makalkalewa mazajensu.
A sakamakon hakan kuma sai sha'awarsu ta motsa sai kuma a shiga jima'i. Don haka a kullum idan za ayi sanyi ma'aurata su kwanta tare a kullum sai sunyi jima'i. Koda sanyi AC ne yai wa mace yawa ya ratsa mata fata, burinta kawai taji ta rungumi namiji koda kuwa ba jima'i zasu yi ba. Shi kuma bamiji rungumarsa keda wuya zai motsa. Motsawarsa keda wuya zai bukaci jima'i. Sai ake ganin kamar maza sunfi jaraba lokacin sanyi ba haka bane.
A lokacin sanyi mata masu tsafta sunfi kula da jikinsu. Hakan yasa fatarsu take yin kyau da kyallen da ke sa jikinsu yayi laushi. Yadda da zaran ta kusanci mijinta sai taushin jikinta ya debeshi. Sai runguma, sai sha'awa ya motsa.
A lokacin sanyi mata sunfi maza samun koshin lafiya a cewar bincike. Wannan lafiyan dake gudana a jikinsu sanyi na shigansu sai sha'awarsu ya motsa. Sai kokarin rungumar miji, daga nan kuma sai a warware mata sanyi.
Mace koda mara batada aure a lokacin sanyi tana bukatar samun wani abu ta runguma koda kuwa filone. Akasarin mata sun fi tunanin yin aure a lokacin sanyi. Hakan yasa jarabarsu ke tashi koda kuwa basu da aure. Daga nan sai neman abunda zata runguma taji dumi koda kuwa kenwarta ce.
💯
ReplyDelete