Dalilin Da Yasa Mata Suka Fi Maza Son Cin Kayan Makulashe

Dalilin Da Yasa Mata Suka Fi Maza Son Cin Kayan Makulashe
Dalilin Da Yasa Mata Suka Fi Maza Son Cin Kayan Makulashe


Ra'ayoyin Matasa Kan Dalilin Da Yasa Mata Suka Fi Maza Son Cin Kayan Makulashe


Ana samun mata da yawa suna da kwadayin ci ko shan kayan Makulashe irin kayan marmari kamar soyayyun kaji ko nama da gasassun kifi ko farfesu. Sannan akwai kayan zaki irin su alawowin caculate, biscuits, alkaki da sauran kayan Makulashe da dama wanda baza mu iya kawo muku sunayen su duka ba.


Hakan yasa muka ji ra'ayoyi daga wajen matasa samari da su kansu yan matan da suke son ci da shan kayan Makulashe. Kusan kowane ya bayyana ra'ayinsa da kuma dalilin da yasa mata suka fi maza son ci da shan kayan Makulashe. Ga ra'ayoyinsu kamar haka;


Kabir Muhammad, yace abinda yasa mata suka fi maza so da cin kayan makulashe saboda siya musu ake yi ba da kudinsu suke saya ba. Amma idan mace ne za ta siya da kudinta ba za ta iya siya ba.


Maryam Saleh, tace ai su mata yan ala-baku musamu ne, ai maza su suke zuwa su Nemo mana kudin kuma mufi su jindadin kudin. Domin kuwa ko saurayina baya iya cin abinda yake sayo min.


Sagir Umar, ai su mata iyayen kwadayi ne idan ba su ci ko shan irin wannan kayan makulashe ba hankalinsu baya kwantawa. Mu kuma maza ba'a san mu da kwadayi irin na makulashe ba, cewar sa.


Yusif Kabir, ai abinda yasa mata suka fi maza ci da shan kayan Makulashe saboda yafi musu amfani a jikinsu fiye da maza, idan maza suna ci ko shan irin kayan kwadayi da mata ke ci ai zai iya yi mana illa, su kuwa mata amfani mai zai musu a jiki.


Bashir Umar, tsarin halittar ba daya bane, yanda namiji zaiji sha'awar kayan Makulashe ya hakura ita mace ba haka bane. Suna bukatar kulawa matuka shiyasa yana da muhimmanci a dinga kulawa dasu yadda ya kamata.


Wadannan dai sune ra'ayoyin wasu daga cikin matasa da muka tattaro muku akan dalilin da yasa mata suka fi maza son cin kayan makulashe. Shin kuna da wasu ra'ayoyin da za ku iya bayyana mana? Ku ajiye ra'ayoyin ku a kasan comment.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post