Dalilin Da Yasa Hukumar Hisbah take neman fitattun yan Tiktok su 6 a Kano

Dalilin Da Yasa Hukumar Hisbah take neman fitattun yan Tiktok su 6 a Kano


 Dalilin Da Yasa Hukumar Hisbah take neman fitattun yan Tiktok su 6 a Kano


Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta tabbatar da sanarwar neman wasu shahararrun masu amfani da shafin Tiktok su 6 saboda furta kalaman batsa cikin wasu bidiyo da suka yi, lamarin da ya ci karo da dokar tabbatar da tarbiyya.


Shugaban hukumar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa ya shaida wa BBC cewa cikin masu amfani da shafin da ake nema akwai Abubakar Ibrahim da aka fi sani da Gfresh sai Sadiya Haruna da Ashiru Idris da aka fi sani da Maiwushirya da Ummee Shakira da Murja Ibrahim Kunya da kuma Hassan Makeup.


A cewar Sheikh Daurawa, suna cigiyar mutanen ne bayan ɓullar wani bidiyo da a ciki suke furta kalaman da ba su dace ba wanda kuma ya ci karo da alkawarin da suka yi lokacin da aka kama su a karon farko domin yi musu wa'azi.


Ya ce babban burin Hisbah shi ne ta ga an gyara kura-kurai tun da "ba so muke mu ci gaba da gayyato mutanen ba, watakila hakan zai sa su ji cewa ba su kyauta ba tun da an yi yarjejeniya da su, sun yi mana alkawari za su gyara [amma hakan ba ta faru ba]."


Sheikh Daurawa ya ce kasancewar wannan ne karo na biyu da suke saba dokar ta tarbiyya, ko da sun bayyana a gaban Hisbah, za su sake jan hankalinsu a kan yin irin wadannan dabi'u tare da tabbatar da cewa sun rubuta alkawarin riko da yarjejeniyar da aka yi da su.


Ya ce sai mutum ya taka doka sau uku sannan ake gurfanar da shi a gaban kotu.


"Ba kotu za mu kai su ba yanzu, ai yarjejeniya sau uku ake yi, idan suka zo, za mu ce musu ya muka yi yarjejeniya da ku, bayan kun gaya mana ba za ku sake ba kuma kuka sake, sai mu ji uzirinsu." in ji Sheikh Daurawa.


Shugaban hukumar ta Hisbah ya ce a baya, sun tattauna da jami'ai daga ofishin Tiktok da ke Legas inda kuma suka ce idan aka samu masu amfani da Tiktok da yake saba doka ko jayo tashin hankali ko ɓata addini "idan muka rubuta muka kai musu, suka bayar da rahoto, za a iya toshe [shafinsa]."


"Wannan ma ya fi yi wa dan Tiktok zafi, ka sa a goge shafinsa domin wani ya tara mabiya da yawa, idan ya ji za a rufe shafinsa saboda gwamnati ta shigo, kuma doka ya karya." in ji Daurawa.


A shekarar da ta gabata ne hukumar ta Hisbah ta gana da yan Tiktok a Kano domin tattaunawa da su game da yadda za a tabbatar da kyawawan dabi'u tare da kawar da fitsara a shafin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post