Dalilan Dake Saka Mace Kauracewa Kwanciyar Jima'i Da Mijinta - Android Pols

Dalilan Dake Saka Mace Kauracewa Kwanciyar Jima'i Da Mijinta
Dalilan Dake Saka Mace Kauracewa Kwanciyar Jima'i Da Mijinta 


Mata da dama na matukar yin korafi akan yanayin da mazajen su ke kusantar su, wani yana iya kwanaki bai yi wanka ba da brush tsawon lokaci 


Duba da yadda maza ke yawan korafin matan su na kin amsa bakatar su a kwanciyar Jima'i yasa naga ya dace a sanar da maza dan sanin dalilan da ke jawo hakan da kuma hanyar gyara dan samun daidaito a tsakani. 


1. RASHIN TSABTAR JIKI :- wari, tsami ko karni na hana zuciya samun sukuni wajen kusantar mai matsalar, ga shi abune mai matukar wuya sanar da mutum ya dinga yin gyara ko tsabtace jikin sa. Mata da dama na matukar yin korafi akan yanayin da mazajen su ke kusantar su, wani yana iya kwana da kwanaki bai yi wanka ba, brush tun safe sai wani safiyar, zai wuni a waje cikin zafi da gumi, ya dawo ba gyara jiki haka zai nemi matarsa, a hakan yana tsammanin mace ta kusance shi cikin aminci.

Shiyasa zakaji "banda kiss" ko bata responding kummmmmm zakaji ko numfashi kamar batayi, ko tana kauda kai, ko ka yi jimai da ita ba dadi za ta ji ba domin tana kyamarka a lokacin saboda rashin tsaftar ka. 

Seriously, gyaran jiki tilas ne a wajen ku kuma. Askin sama da kasa, gyaran kumba, goge faso, wanka akalla sau 2, brush atleast 3×, in zaka kusanceta kuma kana bukatar ku yi kiss brush ya zama tilas.


2. RASHIN WASA KO IYA WASA :- Dabi'ar mace da namiji akwai banbanci a wannan fanni, naturally mace tafi bukatar lokaci wajen wasanni, asalima wasu matan yafi musu asalin jin dadi. A cikin yin wasa da sanin yadda za'ayi wasan anan asalin samar da ni'ima, jin dadi da cikakken gamsuwa yake.   

Matukar za ku tsallake wannan matakin dole ka rasa ni'imarta da hadin kanta, wata ma sai dai zafi da za ta ji, ko sai kun kara da lub wadda shi kuma dadin sa bai kai gardin asalin halittar ni'imar mace ba. Ku sani ko wace mace da yanayinta da abunda ake mata taji dadi. Ka San na matarka, karka manta in bawasa ko baka iya wasa ba dole tana gujema kiranka. 


3. RASHIN SAMUN GAMSUWA :- matukar iyalinka bata samun gamsuwa idan ka kusanceta, tabbas za ta soma gujema shimfidarka domin bata samun abinda take bukata daga gareka. Yi kokari wajen gamsar da ita kafun ka shigeta, ko ka dakata kafun ka kawo kayi wasa da ita.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post