Dalilan Da Suke Motsa Sha'awar Mace Da Namiji |
An Bayyana Dalilan dake motsa sha'awar saurayi da budurwa
Masana sun bayyana wasu abubuwa da suke motsa sha'awar mace da namiji musamman wadanda ba su yi aure ba. Sannan kuma sun bayyana matakan kare kai daga abinda ke motsa sha'awar matasa.
Dalilan Da Suke Motsa Sha'awar Mace Da Namiji
1 tunani na bazato, wato haka kawai tunanin mace ko nami yafado a rai cikin yanayin da sha'awa zata motsa koda mutum bai niyya ba sai yaji sha'awa ta motsa.
2 tunani na ganin dama wato shine mutum ya dinga tunaning mace ko, mace tayi tunanin namiji a yanayin da zai motsa sha'awa bisa niyar tada sha'awar
3 faruwar wasu abu ba tare da niyya ba, kamar jin kalamai masu motsa sha'awa ba bisa niyyaba hada ido da mace ko namiji a shiga ta motsa shawa'a.
4 tsokano sha'awa bisa niyar tada ita kamar kallon mace matsananci ko namiji ga mace, kallon hotuna, finafinai, cakudedeniyar da zata iya tada sha'awa tsakanin mace da namiji.
5 motsawar sinadarai akwai sinadarai da suke samuwa a jikin dan adam matukar wadannan sanadaran sun samu ajikin mutum mace ko namiji to sha'awarsa zata motsa ko yaso ko baisoba.
Sannan sha'awar kowanne mutum Allah (SWT) ya halicceshi da ita mataki mataki. Wani saurayin ma sai a dauka bashi da lafıya dan bashi da wata sha'awa da ake ganin alamarta a tare dashi matsananciya.
Wani saurayin Allah yabashi ita da yawa, yakan shiga mawuyacin hali, balaifine ba dan mutum yayi sha'awa domin dabi'a ce ta dan adam haka kuma Allah ya halicci mutum da ita, kamar yadda dan adam yake jin yunwa idan baici abunci ba, to haka ma sha'awa take motsawa dan adam idan wasu dalilai suka faru na motsawarta.
A Jikin kwakwalwa a kwai wani bangare da ake ce masa cerebrum (a yaren kimiyya) yana dauke da thalamus a wannan gurun ne ake samar da sanadaran da suke haddasa sha'awa. Idan kwakwalwa taso motsa sha'awa idan ma sakamakon tunani ko haka kawai sai wannan bangaren ya bada umarni a samar da sanadarai a jiki wato sexual stimulation hormone, sukuma zasu zaburarda wasu sassa ajikin dan adam su canja daga yanayin na daidai normal stage. Wadannan sassa na dan adam akwai wani mataki na zabura da idan suka kai to bazasu koma daidai ba har sai sha'awa ta biya.
A wannan yanayi sinadari na kunya sukan zama basa aiki sosai (slow down). matsananciyar sha'awa tana zuwa ne lokacin da saurayi ko budurwa suke farkon balaga. Farkon balaga shine lokaci mafi hatsari ga saurayi da budurwa. Saurayi bashi da wani buri a irin wannan lokacin irin ya kashe sha'awar sa ta jinsi, hakama mace.
Samari da yan mata sukan Kwashe 24 hours Zuciyarsu akwai tunani ko hira wacce take da alakar kashe sha'awa, kullum tunanin su wai me ake ji ne. Shin ko ita yaushe za ta fara. A Lokacin balagar farko lallai iyaye su kula da yaransu sosai kuma ku tausaya musu idan suka cika sharadin aure ku yi musu aure shine mafi alheri.
A wannan lokacin fada, duka, ko tsare budurwa a gida a hanata shira da saurayi ba shine dabara ba, domin idan an hanata fita ba kasan mai take aikatawa a daki ko bandaki ba, da fatan za'a kula. Domin duk fada da nasiha ba za su daina jin sha'awa ba.