Bana son auren mace mai tarbiyya nafi son fitinanniya - Al'amin G-Fresh |
Fitaccen dan Titok G-Fresh Al'amin ya ce ba ya son auren mace mai tarbiyya, ya fi son wacce take babu yabo babu fallasa.
Tabbas a Rayuwa ta banason naga anyi aure ace ana samun matsala, saidai kamar yanda kowa dadama sunsan G FRESH AL'AMIN sun san cewa ya auri (sadiya haruna)wacce tsohuwar yar film ce kuma mai saida maganin mata,har akayi auren aka Basu shawarwari cewa abubuwan dasuke yi tik tok yakamata susani rayuwar aure ba rayuwar tasha bace.
Sai gashi yanzun Sunfito suna tonama kansu asiri,kuma suna cece kuce a tsakanin su,kuma a matsayin su na ma'aurata wanda hakan yasanya wasu nata ganin daman irin wannan auren baya lasting,auren yan duniya, saidai akwai kalubale a tarayyar su, dukkanin su basajin kunyar fadin magana ma duniya,irin wannan rayuwar daman Musulunci ya karantar damu cewa duk wanda baiji tsoron Allah akan abinda yakeyi ba tabbas zai dinga ganin jarabawa daban daban, wannan aure nasu aure ne mai cike da rashin kunya,da tarbiyya ga dukkanin su.
Wannan yasanya kowa keta maida musu da martani komadai menene, sunbar abin kunya, saboda sau tari ina yawan maimaita cewa,babu yanda za'ayi ku hadu da mace a kwalta,kuma kuyi aure, kuma kayi tunanin samun zaman lafiya, tabbas auren tasha ko yayi lasting a farko daga karshe saiya watse, saboda tun asalin sa ba'a ginasa a turbar Allah ba, tabbas akwai darasi gameda auren wainnan yan duniyar wallahi.