Bambancin Girman Nono A Tsakanin Mata

Bambancin Girman Nono A Tsakanin Mata
Bambancin Girman Nono A Tsakanin Mata


Yadda Bambancin Girman Nono A Tsakanin Mata yake 


Taswirar girma, zubi da tsari na Nonon Mace ya ta'allakane ga zubin jigidar halittar ta na gado (genetically) wanda shiyasa duk ƴan gida ko ƴan ɗaki ɗaya da wuya kaga ba irin zubin nonon su guda ba, zai wahala.


A nan ina magana ne akan Nono karan kansa. Bawai batun Nono ɗaya yafi ɗaya ba, wannan nasha faɗa is normal asami hakan ai ɗarin bawani significant bane can. 


Sai dai a game da zubin duk nonuwan: Mu sani

1. Yanayi na gado (Heriditary) 

2. Shekarun Mace (Age) 

3. Yanayin cimar da Mace ke samu (Nutrition) 

4. Adadin haihuwar da tai

5. Shayarwarta

6. Samuwar Juna biyu da kuma, 

7. Yanayin yadda jiki ke samarwa da kuma sarrafa sinadarin estyrogin dake mamaye cigaban ƴan matantakarta


Duk waɗannan Abubuwan 7 kowanne ɗaya nada tasiri game da yadda zubin Nononta zai ko kuwa ya kasance.

- Haka zalika girman nono ka iya canzawa lokacin haila, ana iya ganin sun kara tasowa saboda a lokacin estrogen ya hauhawa, don haka ana iya ganin haka a Mace ya zamto lokaci-lokaci kaga kamar nono din na canjawa.

- Hakama lokacin goyon ciki wato juna biyu girmansu kan ƙaru da kuma bayan haihuwa yayin shayarwa.

- Wani lokacin Zubin nada alaka ga ƙibar Mace da kuma yanayin motsawar sha'awa duk sukan canza.

- Haka kuma cimar Mace, idan Mace bata samun isashshen abinci ko me inganci toh hakan zaisa jikinta yake kone kitsenta domin samar mata da kuzari kadda ta cutu, toh nono shi kuma dama wadace yake da kitse (fats) wanda a karshe wannan fats din na daga wanda zai zaizaye domin hanta ta sami abinda zata sama.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post