Auren Kasaita: Saurayi Zai Auri Mata 3 A Rana Daya A Benue

Auren Kasaita: Saurayi Zai Auri Mata 3 A Rana Daya A Benue
Saurayi Zai Auri Mata 3 A Rana Daya A Benue


Saurayi Zai Auri Mata 3 A Rana Daya A Benue


Wani dan Najeriya mai suna Tersugh Aondona ya shirya auran mata 3 a rana guda a jihar Benue. Kamar yadda sanarwa auren ta nuna za'a ayi bikin ne a ranar Laraba 31, ga watan January 2024 a babbar makarantar secondary school ta Jato Aka dake karamar hukumar kwande na jihar. 


An bayyana sunan matan da Tersugh zai angwance dasu, akwai Blessing, Nancy da Sulumshima. Sannan za'a yi shagalin bikin tun daga karfe 6 Na yamma har zuwa safiya, kamar yadda shafin Jaridar Punch suka rawaito. 


Haryy Nyam wanda shine ya fara sanar da labarin auren a shafinsa na Facebook a ranar 31/1/2024 cewa sun shirya tsaf done ziyartar bikin abokinsu Tersugh Aondona Aka. 


 Na iso garin da za'a daura auren wanda za'a yi bikin auren da ba'a tabarruji yin irinsa a jihar ba. Ina tayaka murna tate da matanka, ka yi dace samun mata, ni Kuma sai yaushe ?🥺"


Mutane da yawa na ta bayyana ra'ayoyinsu kan wannan auren da saurayi zai yi da mata 3 kuma a rana daya a lokaci guda. Ba kasafai ake samun irin hakan ba musamman a Najeriya. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post