Amfanin Tafarnuwa ga azzakari |
Amfanin Tafarnuwa ga azzakari: yawan cin tafarnuwa na taimakawa namiji Karin kuzari da karfin mazakuta
Tafarnuwa ta kasance ɗaya daga cikin kayan mahadi na dafa abinci ko magani da aka fi sani a kowane gida. Domin tanada abubuwan ban mamaki na amfani da ake yi na yau da kullum. Babban darajar sinadirai da kayan magani na tafarnuwa shine tana iya warkar da cututtukan jijiyoyin jini da na numfashi da yawa a jikin dan adam.
Kuma kunsan mene, ba iya wannan bane! Yin amfani da tafarnuwa har ma yana iya taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin mazakuta. Matsalar rashin karfin mazakuta lamari ne na sirri wanda zai iya sa rayuwarku ta zama damuwa da takaici. Amma lokaci ya yi da za ku yi bankwana da matsalolin rashin karfin mazakuta domin amfanin tafarnuwa ga azzakari idan kuna amfani da ita.
Wani bincike na Cibiyar Kiwon Lafiya ta Jami’ar Rochester ya gano, tafarnuwa tana dauke da furotin, mai, carbohydrates, fiber da ma’adanai masu mahimmanci kamar iron, calcium, potassium, phosphorus, potassium, da bitamin B6 da C.
Anan akwai bayanai masu ban sha'awa ga duk mazajen da ke neman hanyoyin dabi'a don magance matsalolin mazakuta. Ku sani yin amfani da afarnuwa ga azzakari na warware muku matsalar mazakuta.
Amfanin Tafarnuwa ga azzakari
Bincike ya gano cewa tafarnuwa na da sinadarin da ake kira Allicin wanda ke kara habaka kwararar jini zuwa ga azzakari sosai. Wannan na iya kara karfin mazakuta da kara karfin sha’awar jima’i. Maza masu matsalar rashin karfin azzakari, suna iya yin amfani da tafarnuwa guda biyu zuwa uku kowace rana don cin. Ana iya ci danye ko kuma a saka shi a abinci bayan an gasa shi.
Idan za ku yawaita cin tafarnuwa a cikin abinci tana taimakawa wajen magance matsalar rashin karfin mazakuta ga namiji. Cin tafarnuwa tana taimakawa karawa namiji Kuzari da Karin karfin azzakari. Duk namijin da yasa amfanin Tafarnuwa ga azzakari ba zai yi wasa da ita ba.
Allah ya saka da Alkhairi.
ReplyDeleteMay Almighty Allah bless
ReplyDeleteAllah ya saka da Alkhairi
ReplyDelete