Amfanin cin Kwai ga maza kafin kwanciyar bacci

Amfanin cin Kwai ga maza kafin kwanciyar bacci
Amfanin Kwai 


Me Yasa Maza za Suci Kwai Kafin Su kwanta bacci? 


An san Kwai a matsayin wani abinci dake da amfanin lafiya. Kwai na dauke da sinadarin gina jiki na protein, amino acids da kuma vitamins. Mutane da yawa kan ci Kwai da safe a matsayin wani mahadi na breakfast. A wannan rubutun zan sanar daku amfanin cin Kwai kafin kwanciya bacci. 


Amfanin cin Kwai ga maza kafin kwanciyar bacci 

Da yawa daga cikin maza ba su san fa'ida da amfanin cin kwai kafin kwanciya bacci ba.


1) Masana sun ce cin kwai na daya daga cikin sirrin samun kyakkyawan bacci. 


2) Maza masu fama da matsalar rashin barci ko kuma waɗanda ke fama don samun barci mai kyau a kai a kai ya kamata su ci ƙwai kafin su kwanta.  


3) Ana samun Melatonin a cikin farin kwai, wanda ke taimaka wa jiki yin shiri don kwanciya barci kuma yana sa barci.


4) Kwai yana dauke da sinadarin amino acid, waɗanda ke taimaka wa  kyawun bacci da yin bacci mai tsayi. 


5) Sunadaran da ke cikin ƙwai, a cewar Sharon Natoli, ƙwararriyar likita a Australiya, yana daga cikin masanin abinci mai gina jiki, yace Kwai yana taimakawa wajen ƙara tsawon lokacin barci. 


6) Samun isasshen barci yana taimakawa wajen rage haɗarin cututtukan zuciya, hawan jini, ciwon sukari, da gyaran jiki.


7) Samun barci mai kyau a dare yana da mahimmanci kuma saboda yana taimakawa budewar kwakwalwa, ƙwarewar warware matsala, da kuma kulawa.


Wannan shine amfanin cin Kwai ga lafiyar jikin dan adam kafin kwanciya bacci kamar yadda masana suka bayyana, da fatan al'umma sun ilimantu da wadannan abubuwan. Allah ya kara mana lafiya da imani amin. 


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post