Ali Nuhu Da Murja Kunya Na Cikin Mutane 150 Ma Fi Tasiri A Intanet A 2023
Wata kungiyar kudancin Nijeriya mai zakulo manyan masu tasiri a kafafen sada zumunta a duk shekara mai suna TheJoY150.
Ta zayyana sunayen jarumin fina finan Hausa Ali Nuhu da kuma Murja Ibrahim Kunya a cikin jerin mutane 150 da suka fi tasiri ko suka fi bayar da nishadi a cikin shekarar 2023 da ta gabata.
Daga cikin yan arewacin Nijeriya da suka samu shiga wannan jadawali akwai.
Ali Nuhu, Murja Kunya, Nasiruddin Abdulmumin, Rahama Sadau, Ireti Kingibe, Abdallah Uba Adamu, Auwal Musa Rafsanjani, Natasha Akpoti da kuma Bishop Matheu Hassan Kukah.
A duk shekara kungiyar takan zakulo manyan mutane wadanda take ganin sunfi bayar da gudunmawa a kafofin sada zumunta ta hanyar Nishadantarwa ko Ilimantarwa.