Alamomin Tashin Alkiyama Na Gaskiya

Alamomin Tashin Alkiyama Na Gaskiya
Alamomin Tashin Alkiyama Na Gaskiya 


Yadda Ake Gane Alamomin Tashin Alkiyama Na Gaskiya 

Tashin alkiyama gaskiya ne kuma duk musulmi ya yadda da hakan, amma ana samun wasu suna fadin abinda ba hakan bane, hakan yasa muka kawo muku alamomin na gaskiya. 


Alamomin tashin alkiyama sun kasu zuwa kashi biyu 2 sune;


1- Kananan Alamomi

2 Manyan Alamomi.


Kananan Alamomin Tashin Alkiyama 

Kuma Kananan Alamomin nan zamu iya cewa kaso 90 cikin 100 wallahi sun riga sun bayyana karara, ko kuma sama da haka. Kuma wadannan alamomi kanana sun fara bayyana ne tun aiko Annabi Muhammad SAW sannan zasu cigaba da faruwa har zuwa ga wata wuta da zata fito daga Kasar "YEMAN" zata kora mutane zuwa kasar da za'a tara su daf da tashin Alqiyama.


Daga Cikin Kananun Alamomin Tashin Al-'kiyama sune kamar haka;


1- Aiko Annabi Muhammad SAW a matsayin Annabi kuma Manzo.


Kamar yadda ya fada a cikin hadithin sa cewa; "An aiko ni da tashin Al-'kiyama kamar haka." Sai ya nuna yatsan sa guda biyu (Sabbaha da Wus'dah).


2- Mutuwar Annabi SAW.


Yau kuwa ana magana Shekara dubu daya da dari hudu da wani abu da rasuwar sa.


3- Fitowar wata wuta daga Hijaaz. Wannan wuta kuwa ta fito a Shekara ta 604H. Ka duba littafın "AT-TAZHKIRA FEE AHWALIL MAUTA WA UMURUL AKHIRAH" na Imam Qurtabi shafi na (721- 722).


4- Cin Nasarar yakim Sahabbai na Masallacin Baitul Qudus. Kuma anci wannan yakin na Masallacin a jograncin Sahabin Manzon Allah SAW Umar-farooq bn Khaddab RA a shekara ta goma sha biyar bayan Hijrah. (15H)


5- Cuta zata sauka a Al'umma zata rika kashe su. Kuma munga irin wannan cututtuka da suka bayyana kamarsu;


Kanjamau

Kwalara

Ebola

Zazzabin Maleria, da sauransu 


6- Wata fitana zata shiga gidan ko wani Musulmi wato Talabijin


- Wayar Sadarwa

- Radiyo

- Na'ura mai kwakwalwa da sauransu 


7- Yawaita Kisan kai a Duniya gaba daya. Manzon Allah S.A.W yace; " Duniya bazata tashi ba sai an yawaita (ALHARJ), sai Sahabbai sukace menene ALHARJ sai Manzon Allah yace shine "Kisan Kisa". Bukhari (15/712), Muslim (18/13). Jama'ah ku dibi yanda ake kisa a Duniya, A kasar nan Najeriya haka ake ta kashe muatene basu jiba basu gani ba.


 - ku dubi yakin Duniya da akayi na daya da na biyu har zuwa na karshe, ku duba irin Miliyoyin mutanen da aka kashe.


- Ku dubi kungiyoyin 'yan ta'adda na Duniya yanda suke kashe al'umma ba dare ba rana. Duka wannan alamomi ne dake nuna 'karshen Duniya (tashin kiyama).


8- Wanda aka kashe bai san dalilin dayasa aka kashe shi ba, shima mai kashewan bai san dalilin kisan ba.


- Wannan ko ya faru kowa yana gani, ta yadda ake sa mana Bama-bamai a masallatai, kasuwanni, da Makarantu, da Tashan motoci da sauransu. Mutane basu da laifın komai basu san me sukayi ba basu san komai ba sai kawai a kashe su ba gaira ba dalili. To wannan alamar tashin Al-qiyama ne.


9- Yanke Zumunta.

Wannan shima yana faruwa da yawa kowa ya sani kuma ya gani. Abin bakin cikin ma shine yanda mutane basa bukatar ma a ziyarce su, saboda tunanin za'a sami wani abu a hannun su.


10- Za'a ha'inci Amintacce


11- Za'a amince wa Maha'inci.


12- Wasu Shugabanni zasu bayyana zasu rika yin magana ba wanda zai musanta.


Mabiyan zasu rika yi musu makauniyar biyayya zasu ri'ka amsar umarnin su suna aikatawa babu ruwan su da cewa umarnin ya saba Allah da Manzonsa, sunayi musu makauniyar biyayya. Wannan ma alamar tashin Duniya ne yazo.


14- Za'a maida Masallaci ya zama hanya. Shine kaga kawai mutane basa sallah a ciki sai dai a zo shiga bayin Masallaci su biya bukatar su Su wuce ba za suyi sallah ba. Ko kuma su maida Masallacin wajen taro kawai sai dai ayi a gama a fita.


15- Za'a yawaita kasuwanci, Mata zasu zama 'yan kasuwa haka maza 'yan kasuwa zasu karu. Yanda zaka gane Duniya tazo karshe, Mata har fita kasar waje sukeyi don siyo kayayyaki su siyar, irin su Dubai Chaina Japan Saudiyya da sauransu , duka wannan alamar tashin Al-'kiyama ce.


16- Za'a yawaita jami'an tsaro. Idan kuwa kayi tunani zakaga hakanan, Musamman a kasar nan, Munada;


- Sojan Kasa

- Sojan ruwa

- Sojan Sama

- 'yan Sanda

- 'yan Sandan Farin kaya

- Road Safety

- Custom

- V.I.O

- Immigration da sauransu, masu kaki zasuyi yawa.


17- Limancin Yara kanana saboda sunada Murya mai dadi ba don cewa Masana bane.


18- Dukiyar Musulmai (Ta kasa) ta zama Ganima ga tsirarun mutane.


- Ma'ana: Wasu Shugabanni su damke kudin kasa su maida shi na kashe mu raba tsakanin su da iyalan su basu damu da halin da Talakawan su ke ciki ba.


19- Zakkah ta kasance ana hanawa. Hakan zai kasance ne za'a rika hana da yawan Musulmai zakkah, sai dai a bama wadanda suka wadata da ita saboda neman suna, ko kuma abin Duniya.


20- Mutum yayi biyayya ga Matarsa ya cutar da Mahaifiyarsa. Subhanallah.! Irin Wannan sharrin yanzu haka shi yake faruwa a Duniya a halin yanzu. Ko da kuwa mutum zai yima matarsa wani abu sai kuma yayi ma mahaifıyarsa to shima ya shiga ciki.


Ana son komai ya fara gabatar dashi ga Mahaifiya kafın kowa. Allah ta'ala muke roko yasa mu cika da Imani.


Wannan sune alamomi tashin alkiyama, amma suna dayawa sosai kawai dai mun takaita ne don Kada rubutun yai tsayi da yawa.  In shaa Allahu zamu kawo su daya bayan daya anan gaba idan Allah yaso.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post