Alamomin shigar ciki a satin farko |
Alamomin Yadda mata za su gane shigar ciki a satin farko
Samun ciki babban abin farin ciki ne ga mata da yawa, amma zai iya zama kuma wani abu mai wahala da kuma damuwa. Daya daga cikin tambayoyin da mata ke yi shine wasu alamomi ne da zasu gane shigar ciki a satin farko. A wannan topic, zamu duba wasu daga cikin alamomin da mata za su iya ganewa a makon farko na shigar ciki.
Wani bincike ya gano cewa da yawa daga cikin mata idan sun samu ciki ba kasafai suke ganin wasu alamomi a satin farko ba, amma wasu suna ganin alamomin kamar rashin lafiya, ciwon nono, da kuma ciwon ciki mai nauyi a cikin kwanaki 5-6 bayan jima’i.
Masana ilimi na lafiya sun bayyana cewa mata suna iya gane shigar ciki a satin farko idan suka yi laakari da yin al'adar su na karshe. Amma wannan topic zai yi bayani alamomin na zahiri da za ku yi saurin ganewa.
Missin din kwanakin yin period shi ne babban alama na farkon da mace za ta iya gane ta samu ciki. Wasu daga cikin alamomin shigar cikin na satin farko sun hada da:
Alamomin shigar ciki a satin farko
Ciwon ciki tare da ko ba tare da ɗaukar magani
Canjin nono, kamar ciwon nono, kumburin nono,
Tashin zuciya da jin alamun kumallo
Yawan sha ruwa
Yawan fitsari
Ciwo kai
Sama da ƙarfin jini na ƙai
Kumburin ciki da yin gyatsa
Rashin lafiya ko rashin ƙarfin jiki
Zargi ko canji a halin zuciya
Yana da muhimmanci a lura cewa ba a fiya ganin wadannan alamomin shigar ciki a satin farko ba. Hanya mafi sauki da mace za ta gane tana da juna biyu shine taje ai mata gwaji a asibiti.
A ƙarshe, makon farko na shigar ciki shi ne lokaci mai muhimmanci ga mai cikin da kuma abinda ke cikinta. Yayin da yawan mata ba su ganin wasu alamomi gane suna da ciki a wannan lokacin, wasu kuma zasu iya samun alamomin shigar ciki kamar rashin lafiya, ciwon nono, da kuma ciwon ciki mai nauyi. Idan kuka ji wannan alamomin zai iya yiwa shigar cikin ne, yana da muhimmanci ku je ku yi gwaji tare da neman shawarar daga wajen likitoci.