Alamomin Samun Juna Biyu |
Alamomin Da Za'a Gane Mace Ta Dauki Juna Biyu, Ko kuma alamomin Shigar Ciki
Ba kowace mace ce ta kwana da sanin cewa babban abin dake kawo batan wata shine samun juna biyu ba. Bayan juna biyu kuma cutukan shigar kwayoyin cuta mahaifa sune kan gaba wajen kawo batan wata, ko rikicewar lissafın wata (haila).
Sauran sun hada da shayarwa, yawan damuwa ko ciwon damuwa, da rashin zama wuri daya ko rashin samun hutu, kamar masu wasanni masu tsanani, wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai walau na asibiti ko na gida.
Alamomin Juna Biyu
Akwai alamomin da mace zasu gane shigar ciki ko samun juna biyu, wasu sunana gane shigar cikin sati uku, wasu kuma suna gane shigar ciki na sati biyu wasu ma har sati daya. Ga dai alamomin samun juna biyu kamar haka;
1) A watannin farko mace za ta yi batan wata, bayan 'yan satuttuka, sai ta fara samun tashin zuciya da sassafe har da amai a wasu lokuta, koda bata ci komai ba. Sauran alamun sun hada da saurin gajiya, idan an yi wani dan aiki ko jin jiri, idan an zo mikewa.
To a wannan lokaci ne ake so a je a yi gwajin juna biyu a tabbatar ta hanyar auna fitsari, a yi hoton ciki, idan ma cikin ne a tabbatar a mahaifa yake ba a waje ba.
2) A watannin da ciki ya fara tsufa kuma, kamar ya kai wata uku, akan ga alamu kamar haka: Girman ciki, yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fıtsari. A wasu akan samu ciwon baya, da ciwon kirji wato zafın kahon zuci ko kwarnafi saboda 'acid' din ciki na tasowa a kirji.
3) Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki, da budewar hanci a wasu da kuma nauyi ko ciwon mama. Ba dole ba ne kowace mace ta samu dukkan wadannan alamomin samun juna biyu ba, amma kusan rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamomin na shigar ciki da muka bayyana. Allah ya saukar da mata masu juna biyu lafıya