Alamomin Rashin Haihuwa Ga Maza

Alamomin Rashin Haihuwa Ga Maza
Alamomin Rashin Haihuwa Ga Maza


Alamomin Rashin Haihuwa Ga Maza


Babbar alamar rashin haihuwa ga maza ita ce namiji ya kasa yiwa mace ciki bayan shafe aƙalla shekara ɗaya yana isashen jima'i da ita.


Amma a wasu lokuta akwai wasu alamomi da ke iya bayyana ga namiji waɗanda suna da alaƙa ne da cutar da ta haddasa masa rashin haihuwa. 


Alamomin Rashin Haihuwa Ga Maza

Waɗannan alamomin sun haɗa da:

1. Matsaloli a wajen jima'i: Waɗannan sun haɗa da rashin fitar da isasshen ruwan maniyyi ko kuma samun wahala wajen fitar da shi, ƙarancin sha'awar mace ko kuma rashin samun ƙwaƙƙwaran miƙewar azzakari.

2. Jin ciwo ko kumburi a cikin 'ya'yan marina

3. Rashin jin ƙamshin komai a hanci

4. Fitowar nono a ƙirjin namiji

5. Rashin fitowar gashi a fuska da kuma sauran sassan jiki.

6. Namiji mai muryar mata

7. Fitar da ƙasa da isasshen ruwan maniyyi (Isasshen maniyyi shi ne wanda ke ɗauke da tantanin halittun haihuwa da basu kasa miliyan goma sha biyar ba (15 million) a duk cikin mil ɗaya na ruwan maniyyin ko kuma miliyan talatin da tara (39 million) a duk ruwan maniyyin da aka kawo cikin inzali ɗaya).

A lura cewa, za'a iya samun mutum da wasu daga cikin alamomin da muka ambata a sama kuma yana haihuwa.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post