Alamomin Namiji Mayaudari

Alamomin Namiji Mayaudari
Alamomin Namiji Mayaudari


Alamomi 10 Da Ake Gane Namiji Mayaudari


'Yan mata da dama suna shiga cikin tarkon shedanun samari su yaudaresu suyi ta zina da su da tunanin zasu auresu saboda rashin sanin wasu tarkon na ma yaudarar maza.


Ga wasu daga cikin alamun da zaki yi sauri da saukin fahimtar saurayin ko namijin da yanzu haka kike soyayya dashi ba aurenki yakeson yi ba zina kawai yake son yi dake.


Alamomin Namiji Mayaudari

1: Zaki ga cewa bai yabon halayenki ko dabi'unki masu kyau kullum maganan halittun jikinki yafı magana maimakon wasu halayenki.


2: Bazai miki maganan aure ba kuma idan kin masa bai daukan zancen da mahimmanci. Duk sanda kikai masa maganar sai ya dinga waskewa. 


3: Yana gudun 'yan uwanki da nashi su ganki. Don haka da wuya ya gabatar dake a wajen wasu na kusa dake kuma zai rika kauce miki idan kika bukaci yaga wasu naki nan ma zai rika zullewa.


4: Mafı yawan lokaci yafı son ki ziyarceshi maimakon shi ya rika zuwa wajenda kike. Duk namijin da kike soyayya dashi har idan ba zai zo gidanku ba Kada ki kuskura ya gayyaceki wani wajen domin yaudarar ki zai yi. 


5: Yana son gayyatarki wuraren shakatawa da holewa maimakon wajen da zaki samu karuwa na addini ko na wani illimin zamani.


6: Wasu alamun shine idan kikayi wani kuskure baya iya fitowa a fili ya nuna miki saboda babu son gaskiya a zuciyarsa kada ranki ya baci.


7: A duk lokacin da kuka kadaita burinsa shine ya tabaki ko ya jawoki a jikinsa. Duk namijin da yake son mace da gaske ba zai dinga taba jikinta ba har sai ya aure ta. 


8: Sakonninsa na waya zantukan batsa da yabon halittarki sunfi yawa maimakon wasu maganganu da zai miki masu mahimmanci.


9: Duk hiran da zaku yi da wuya ya rika zuwa miki da zantunka da zai amfani rayuwanki. Ko hira yadda zai taimaki rayuwanki.


10: Bai damuwa da kokarin saninki, tarihin ki dana zuri'arku. Ko sanin abubuwan da kike burin yi ko zama. Zai ta zuwa miki da zantuka da basu shafi rayuwar auren ku ba hakan yana nuna yaudarar ki kawai zai yi. 


Wadannan sune wasu daga cikin alamomin da mace za ta iya fahimtar saurayin namiji mai sha'awan zina dake mayaudari wanda ba aure ya kawo shi ba. Da fatan idanuwaku zasu bude ku iya fahimtar masu sonku na gaskiya.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post