Alamomin Jinnul Ashiq Da Yadda Mutum Zai Gane Yana Da Aljanin Dare

Alamomin Jinnul Ashiq Da Yadda Mutum Zai Gane Yana Da Aljanin Dare
Alamomin Jinnul Ashiq Da Yadda Mutum Zai Gane Yana Da Aljanin Dare

Alamomin Yadda Mutum Zai Gane Yana Da Aljanin Jinnul Ashiq 


Mutane da yawa na neman sanin menene jinnul ashiq, wane alamomin ne ake iya gane jinnul ashiq ya kama mutum, tayaya mutum zai kare kansa daga fadawa taron jinnul ashiq? 


Wannan sune muhimman tambayoyi na kai tsaye da ake yawan yinsu. Wannan dalilin yasa a yau muka kawo muku alamomin yadda za ku gane jinnul ashiq da matakan kare kai. 


Alamomin Yadda Mutum Zai Gane Yana Da Aljanin Dare (Jinnul Ashiq) 

Akwai alamomin jinnul ashiq na jikin maza akwai kuma na mata, amma bari mu fara da na maza. Gaau kamar haka;


1) Rashin sha'awar aure ko jima'i sam-sam, yana daga cikin alamomin jinnul ashiq kaji baka sha'awar kusantar mace. 


2) Rashin mikewar gaba sanda kai nufın yin jima'i, alhali kuma haka kawai ma yana tashi. Idan kaji irin wannan yanayin kai kokarin daukar mataki. 


3) Kin fitowar ruwa yayin jima'i, domin Aljanin yana iya zama a cikin marainan mutum. Idan kaji baka Iya fitar da maniyyi ko Maziyyi a lokacin saduwa alama ce ta tasirin jinnul ashiq 


4) Saurin gajiya, yayin jima'i da rashin iya komawa, idan kasaba yin Jima'i ba tare da gajiya ba amma kuma daga bisani kaji baka son ka yi, to alamu ne dake nuna tasirin jinnul ashiq. 


5) Jin motsi kamar tafiyar wani abu a gabobin haihuwa yayin jima'i. Shima wannan tasirin jinnul ashiq ne. 


6) Rashin cimma bukatar Jima'i, idan kaji baka bukatar son yin Jima'i da matarka to ka nemi maganin jinnul ashiq. 


7) Idan ka yi nufın yin jima'i sai bacci ya dauke ka. Wannan shima tasirin ashiq ne. 


8) Da ka yi niyyar yin jima'i kawai sai ka ji ka kawo tun kafın ka fara. Tasirin sa ne haddasa maka saurin inzali 


9) komawar gaba da maraina su shige ciki. Zakaga ya'yan maraina sun koma ciki kamar babu su. 


10) Yawan ciwon kai, bacin rai mara dalili, faduwar gaba, da dai sauran su.


11) Haka kawai sai ka ji ka tsani matar ka. Zakaji baka Kaunarta 


12) Yawan mafarki kana saduwa da wata mata. Duk wannan sharrin jinnul ashiq ne 


13- Yawan samun matsaloli a duk inda ka je neman aure, sai maganar ta lalace.


14) Za ka dinga mafarkin wata tana wasa da kai.


15) Matsananciyar sha'awa da tsoron mata. Da dai sauransu.


Alamomin Da Mace Zata Gane Aljani Ya Aure Ta ( alamomin jinnul ashiq a jikin mace) 


1) yawan ciwon ciki mai tsanani da jin motsi acikin.


2) A duk lokacin da sukai nufin saduwa kawai sa ta ga jini ya zo ma ta alhali ba lokacin al'adarta bane.


3) Jin zafı yayin jima'i da rashin samun wata fa'ida. Sannan suna gama jima'i sai maniyyin da mijinta ya zuba ma ta ya dinga dawowa, ba zai shiga mahaifar ta ba ga kuma matsanancin ciwon baya ko kwankwaso.


4) kin yarda da Jima'i. Za ki dinga yawan mafarkin wani na saduwa da ke, da siffar mijinki ko da wata siffa daban.


5) Yawan yin mafarkin kin haihu wataran ma har da taron suna, sannan ganin wani a mafarki ko a fili ya nutsa hannun sa a cikinki ta ya fizgo wani abu, musamman idan kina da ciki.


6) Yawan yin barin ciki ba tare da wani sanannen dalili ba. Sannan kuma da yawan yin mafarkin ana bin ki a guje ko ana kokawa da ke.


7) Jin motsi a cikin ki, wani lokaci ma har yana dada girma, amma idan likitoci suka auna za su ce ba su ga komai ba.


8) Rashin son yin magana da kowa da jin haushin mutane haka kawai.  Sannan kuma za ki dinga tsanar mai gida haka kawai, alhali za ki ji kina sha'awar wasu mazan. Wanna tasirin jinnul ashiq ne. 


9) Jin wari mara dadi yana fito miki ko jin kaikayin gaba da kurajen gaba. Idan budurwa ce, duk wanda ya zo neman aurenta to in ya tafi ba zai dawo ba. Wannan alamomin jinnul ashiq ne. 


10) Idan mutum ya dage yana so ya aureta ita kuma sai ta ji ta tsaneshi. Idan ta fita unguwa zata dinga ganin alamun maza suna so su yi mata magana amma sai su kasa, wasu za su dinga fadar cewa wance kwarjini take yi musu.


11) Za ta dinga yawan zama a duhu da zama ita kadai da rashin son magana da mutane. Idan yarinya tana zuwa makaranta za a ga kokarinta yana raguwa kuma tana ramewa.


Yawan ciwon kai da yin jiri. Sannan kuma ga faduwar gaba, musamman idan Magriba ta kusa. Ko kuma idan mace ta fara barci sai ta ji an zungureta ta farka.


Da dai alamomi da yawa. Mafita shi ne idan kun ji Irin wadannan alamomin na jinnul ashiq ku yi kokarin ku ziyarci mai yin rukiyya don ya dora ku akan tsarin maganin da ya dace da ku. Kuma ku dinga zama da alwala da addu'o'in safiya da maraice.


Idan wannan matsala tayi karfı dole sai an yiwa mutum rukiyyah, an nemi Aljanin an kona shi ko kuma a hada magungunan da za su kashe shi. Amma dai sihiri da Aljani ba su isa su cutar da kai. Dole ku kiyaye sauraren kade-kade da kalle kalle. Kuma dole ku koma tsarin koyarwa addinin musulunci. 


Azkar din da ake yi na safıya da yamma da lokacin kwanciya bacci, indai muka kiyaye cikin ikon Allah za'a samu waraka. Jinnul Ashiq ana rabuwa dasu da iznin Allah. 


GA Wani Ku Hada;

Ku samu wannan abubuwan kamar haka;


1. Garin Habba 

2. Garin Zaitun 

3. Albabunaj 

4. Kusdil Hindi. 

5. Sazabu 

6 Zuma 


Yadda Za'a Hadasu 

A hade su waje guda a dinga dibar kamar cokali 1 ana tafasawa da ruwa, idan ya tafasa sai a zuba Uma a sha kamar shayi, kafin a sha a tofa wannan ayoyin da surorin kamar haka;


Fatiha kafa 3

Ayatul kursiyu 3

Kulya 3

Kulhuwallahu 3

Falaki 3

Nasi 3

A tofa a ciki, zaa sha safe da yamma. Allah ya bamu lafiya da zama lafiya amin. 



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post