Alamomin Da Zaka Gane An Yi Maka Sihiri |
Alamomin Yadda Da Zaka Gane An Yi Maka Sihiri Da Matakan Warwarewa
Yau za mu yi bayani kan alamomin da mutum zai gane an masa sihiri da kuma yadda zai gane akwai sihiri a jikinsa da kuma yadda sihirin ke da tasiri wajen lalata taurarun dan adam sannan kuma da yadda Za'a warware sihirin idan har ya faru da mutum.
Menene Sihiri Kuma Yaya Alamomin Da Ake Gane Sihiri Ne
Abinda ake nufi da sihiri shine shigar wani abu cikin rai, ma'anar rai shine Kurwa wato Spirit a turance kenan, a larabce kuma (Arwah) wato Ruhi, Kurwa ko Arwah ko Spirit kuma itace Taurararin dan'adam guda Tara suke jikinta wato (Stars). Dalilin da zaka ji ana cewa Dan'adam Tara yake bai cika Goma ba ai ma'ana Taurari guda Taran nan da suke cikin Kurwarsa ko ruhinsa su 9 ne, abinda ya kewayesu na goman shine Ajali, toh in aka yiwa mutum sihiri ko sammu ko makaru, nan Sihirin ke zuwa ya zauna cikin kurwarsa ya gurbata Haske da karfın Taurarinsa ta yadda Matsaloli iri iri da kala zasu dinga Faruwa da shi.
Menene Taurari Da Kuma Matsayin Su A Jikin Dan Adam
Abinda ake nufi da tauraro ko taurari na Dan'adam shine, wato a cikin halittar Dan'adam ne cikin ruhinsa ko kurwarsa ko spirit nashi Sai Allah ya zuba masa taurari guda 9 wadanda suke sanadin samuwar duk wata kaddararsa ta farinciki ko bakinciki, samu ko rashi ko akasin haka, kowanne ya danganta da nasabar haskawar daya daga cikin taurari tara dake wakilcin wannan abin.
Ba a ganin taurarin Dan'adam amma akwai wasu daidaikun mutane wadanda Allah ya bude musu gani ba na ido kadai ba, gani na ganin sirrika boyayyu misali gane taurari da yadda suke, da kuma gane duk wata boyayyiyar cuta ko al'amari dake faruwa da mutum.
Nau'in Kalolin Taurari
1. Tauraron so wato Rihatul Hubbi Wanda zaka so a soka
2. Tauraron Aure
3. Tauraron Haihuwa
4. Tauraron Daukaka
5. Tauraron Mulki/Arziki
6. Tauraron Jama'ah
7. Tauraron Farinciki
8. Tauraron llimi
9. Tauraron Lafiya
Wadannan Taurari guda Tara da aka lissafo sune rayuwar mutum da kuma abinda mutum yake rayuwa a cikinsa, Idan aka kulla maka sihiri sai sihirin ya shiga ya zauna a guraben halittar wannan taurarin a cikin ruhinka, sai ya dinga cutar da su yana disashe haskensu ta yadda duk tauraron da ya disashe sai matsala ta dinga faruwa a kan abinda tauraron ke wakilci na rayuwar Dan'adam.
Wadannan taurari guda tara, kowannensu yana Dauke da Gaba-Gaba guda Tara, shiyasa misali wani yafı wani Arziki, saboda wani Tauraronsa na arziki gaba Uku ne ya haska, wani kuma gaba biyar ko fiye, don haka dole me haske gaba biyar ya dara me gaba uku arziki ko Mulki, haka Tauraron haihuwa, wani yafı wani yawan "yaya, haka kuma idan Tauraronka Na arziki gaba daya ya haska toh zaka ga kana shan wahala wajen Neman abinci, kuma baza ka dinga samu ta dadi ba.
Wanda kuma tauraron arzikinsa gaba biyu ne zai dinga samu amma kadan kadan kuma me Saurin karewa, Wanda ya haska gaba uku kuma zai dinga samu akai akai, toh akwai matakin hasken tauraron da ya kai gaba biyar ko fiye, shi Arzikin ne ma zai dinga nemansa ba shine zai dinga Neman Arzikin ba, misali zaiga kowa nemana yake da harkar kudi ba shi yake Neman mutane ba.
Ana iya Haska Taurari Idan Suka Samu matsala ta hanyar aiki na addua da kuma magani a kan Kurwa da tauraron da aka gane ya samu matsalar, wannan a takaice ne nayi bayani Amma bayanin ya ma wuce haka, kawai nah dauki misalin tauraron arzikine sai na dan yi tsokaci don a gane bayanin da kyau.
Yaya Mutum Zai Gane An Yi Masa Sihiri Ko Akwai Sihiri A Jikinsa?
Akwai alamomi da dama da ake gane cewa akwai sihiri a jikin mutum, ga kadan daga ciki zan zayyano su kamar haka;
1. Rikicewar Al'amura ba gaira ba Dalili ya kase gane me ke faruwa da shi? Misali duk abinda ya sa gaba sai yaga yaki yiyuwa kokuma ko ya yiyu sai a samu matsala ta yadda abin zai wargaje daga gunsa ko daga gun abokan Harkarsa.
2. Rashil lafıya wacce bata da dalili ko wacce bata jin magani, ko kuma Ciwon da za a kasa gane Kansa ko a kasa ganinsa a asibiti in anyi gwaje gwaje
3. Rashin barci da Rashin Nutsuwa a zuciya kodayaushe
4. Rashin farinjini a wajen Jama'a da yawan samun matsaloli iri iri a wajen jama'a da ake Hulda da su
5. Faduwar gaba da Rashin cikakkiyar lafıya a koda yaushe
6. Rugujewar Al'amura na Alheri da ake ginawa don cigaban Rayuwa
7. Faruwar abubuwa Marassa dadi da tsautsayi da iftila'i daban daban
8. Mutum ba Neman mata ko shan giya yake yi ba Amma duk abinda ya samu kaman an kona, ya rasa me yayi da shi kuma shi ba neman mata ko shan giya ko chacha yake ba, Amma ko me ya samu zai lalace gaba daya.
A takaice kenan kuma kadan kenan daga cikin alamomin da mutum zai gane akwai sihiri a jikinsa. Mafita shine in aka yiwa mutum Sihiri dole da farko a fara warware SIHIRIN saboda dakatar da tasirin sihirin shine farko sannan gyaran ta'adin da sihirin ya yiwa Taurarin, idan aka karya sihirin amma kuma ba a gyara ta'adin da sihirin ya yiwa taurarin NASA ba toh da matsala, domin zai dauka har wayau matsalar bata kau bane.
Misalin warware sihiri ba tare da an gyara Taurari ba kaman misalin Gobara ce ta kama a gida sai a kashe wutar kuma masu gidan su shiga gidan su zauna ba tare da gyara ba, abubuwa sun kone ba a gyara ba kuma an shiga ana zama gidan shin haka yayi tsari? Kuma shin hakan zai yiyu? Da wahala gaskiya toh kamar hakane.