Alamomin ciki na sati daya

Alamomin ciki na sati daya
Alamomin ciki na sati daya


Shin wadanne alamu mace zata ji ko ta gani idan tana dauke da sabon ciki ta yadda za ta gane tun kafın ta je asibiti?


Akwai wasu alamomi da ake iya gane shigar ciki tun a satin farko, wasu matan suna iya ganewa da yawa kuma basa fahimtar hakan. 


Ba kowace mace ce ta kwana da sanin cewa babban abinda ke kawo batan wata shine samun juna biyu ba. Bayan juna biyu kuma cuttukan shigar kwayoyin cuta mahaifa sune kan gaba wajen kawo batan wata (Rashin ganin period), ko rikicewar lissafın wata.


Sauran abubuwan dake kawo batan wata sun hada da;


Shayarwa, Yawan damuwa ko ciwon damuwa, Rashin zama wuri daya ko Rashin samun hutu, kamar masu wasanni masu tsanani, Wasu lokuta ma har da shan wasu magunguna barkatai walau na asibiti ko na gida.


Alamomin ciki na sati daya

Wadanne alamu mace mai juna biyu za ta ji ta tabbatar ciki ne tun a sti daya?


Gasu nan a zayyane: A watannin farko mace zata yi 6atan wata, bayan yan satuttuka, sai ta fara samun Tashin zuciya da sassafe har da amai a wasu lokuta, koda ma ba'a ci komai ba.


Sauran alamun sun hada da; Saurin gajiya, idan anyi wani dan aiki ko jin jiri (dizziness) idan an zo mikewa, Zub da miyau, Zazzabi, Rashin son kamshin koda turare Ga wasu.


Gwajin Ciki a Sati Daya

To a wanne lokaci ne ake so aje ayi gwajin juna biyu?


A tabbatar ta hanyar auna fitsari, Sannan sai ayi hoton ciki, idan ma cikin ne to ta hanyar hoton za'a tabbatar acikin mahaifa yake ba'a waje ba wato (ectopic pregnancy).


A watannin da ciki ya fara tsufa kuma, kamar ya kai wata 3, akan ga alamu kamar haka: Girman ciki, Yawan jin fitsari ko zaryar yin fitsari, saboda abin da ke ciki ya fara danne marar fitsari.


A wasu akan samu ciwon baya, da Ciwon kirji wato zafın kahon zuci ko kwarnafi saboda 'acid' din ciki na tasowa a kirji.


Sai kuma a fara samun duhun fuska da fitowar zane a fatar ciki, da budewar hanci a wasu da kuma nauyi ko ciwon nonuwa.


Ba dole bane kowace mace ta samu dukkan wadannan alamun ciki a sati daya, amma kusan rabin mata suna samun a kalla rabin wadannan alamun.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post