Alamomin Aljani A jikin Mace |
Alamomin Yadda Mata Za Su Gane Shigar Aljani A jikin Su
Shigar aljani jikin mata yana matukar cutar da lafyiar su, shiyasa wasu matan har su gama rayuwarsu basu yi aure ba saboda aljani ba zai barsu su yi ba. Wasu kuwa sai sun dauki tsawon shekaru kafin a yi nasarar rabata dasu.
Idan aka ce Jinnul Ashiq ana nufin Aljanin da ke zuwar wa mace da daddare yana saduwa da matan mutane, ana kuma samun Aljana mai zuwa da dadddare ta dinga saduwa da namiji.
Su irin wadannan Aljanu suna aurar mace ne ta yadda za su dinga kwanciya da ita a duk lokacin da suka ga dama suna kuma kokarin hana ta aure, idan kuma tana da auren sai su dinga kokarin kashe mata shi. Su na kuma kokarin hana mace samun ciki, ko kuma idan ta samu cikin sai su zubar mata da shi. Sukan ma biyo yaron da matar ta haifa, ya zamo tun daga haifar sa za a ga alamun jinnu a tare da shi. Irin wannan nau'in Aljani shi muke kira
JINNUL ASHIQ ﺟﻦ ﺍﻟﻌﺎﺷﻖ
Alamomin Aljani A jikin Mace
Wani lokacin irin wannan Aljanu suna shiga jikin mace ko namiji ne idan an saka su, wato ta hanyar Sihiri kenan. Wani lokaci kuma gamo ne mutum yake yi da su.
Anan gaba kadan zan yi bayanin alamomin da mace za ta gane Aljani ya aureta ko kuma mamiji ya gane Aljana ta aure shi amma kafin nan ga hayaki da man shafawa da ake amfani da su wajen maganin Jinnul Ashiq na har abada in dai zaka jure amfani dashi na wata 1 duk taurin kan Aljani zai rabu dakai na har abada.
Abubuwan da za'a hada sune kamar haka
1. Bakin hayaki
2. Ganyen magarya
3. Ganyen gamji
4. Haltit
5. Saiwar tumfafiya
Hayaki ajiki ko daki ko gida inshallah zaku sha mamaki. Sannan kuma a dinga karanta Ayatal kursiyyu lokacin da ake hayakin.
Sai kuma man da ake hadawa na shafawa ga jiki sau 2 a rana
1. Man habbatussauda 125ml
2. Man tafarnuwa guda 2
3. Man Gelo 1
4. Miski guda 2
5. Man zaitun 1
6. Turaren zaafaran
7. Turaren wardi
Shike nan, Bawai rabuwa da iska ne ba'a yi ba a'a mutane basu iya jure yin magani kullum. Allah baiwa dukkan musulmai lafiya
Darasin mu na gaba za mu kawo muku alamomin alamomin aljani a jikin mace wanda idan taji su ba sai wani ya fada mata ba ita da kanta zata gano cewa tana dauke da aljani. Da fatan za ku ci gabaki da bibiyarmu.