Addu'ar Rage sha'awa |
Yadda Ake Yin Addu'ar Rage Karfin Sha'awa Don Matasa Marasa Aure
Tambayoyi sun yi yawa daga wajen matasa maza da mata wanda suke neman a yi musu bayani ko kuma a fada musu addu'ar da za su dinga yi domin su rage sha'awa dake damun su.
Dukkanin abin da kaga ya gagareka a rayuwarka, ka kasa samun iko a kansa balle ka mallake shi, to ka yawaita addu'a a kansa, hakika Allah zai isar maka shi"
Addu'ar Rage sha'awa
Idan kana da karfin sha'awa kuma ka kasa mallakar kanka a kanta, to ka yawaita yin addu'ar raguwar ta, hakika Allah zai daidaita maka ita in shaa Allahu
اللَّهُمَّ إِنِّي أَعُوذُ بِكَ مِنْ شَرِّ سَمْعِي وَمِنْ شَرِّ بَصَرِي وَمِنْ شَرِّ لِسَانِي وَمِنْ شَر قَلْبِي وَمِنْ شَرِّ مَنِيِّي
"An sami ruwayar hadisi daga shakali Dan Humaidin yace: na je gurin Manzon Allah, sai nace ya annabin Allah! Ka koya mini yadda zan dinga neman kariya, yace sai ya riki hannuna, yace: kace "Ya Allah ina neman tsarinka daga sharrin jina, da sharrin ganina, da sharrin harshena, da sharrin zuciyata, da kuma sharrin maniyyi na". yana nufın sharrin farjinsa. Jami at-Tirmidhi 3492
Duk wanda yake fama da yawan sha'awa kuma yake son ya rage yawan sha'awar to Kada yai sake da yawaita yin wannan addu'ar zai samu waraka sosai. Sannan idan da halin yin aure to ku yi domin shima maganin rage yawan sha'awa ne.