Abubuwan Dake Sa wankan Janaba

Abubuwan Dake Sa wankan Janaba
Abubuwan Dake Sa wankan Janaba


Wankan Janaba Da Abubuwan Dake Wajabtashi 


Wanka a Shari'ance, Shi ne gama jiki gabadaya da ruwa, a kan wata siffa kebantacciya, da niyyar bautawa Allah Mai tsarki


Abubuwan Dake Wajabta Wankan Janaba 

Malamai sun yi bayani kan wajbacin yin wankan Janaba, ga jerin su kamar haka:


1- Fitar Maniyyi:- Maniyyi wani ruwa ne fari mai kauri, wanda yake fita tare da jin dadi, yana tunkudar juna yayin fitowa, mutuwar jiki tana biyo bayan fitarsa, yana wari irin warin bara-gurbin kwai.


Allah Madaukakin Sarki ya ce, "Idan kun kasance kuna da janaba to ku yi wanka" (Alma'ida : 6)


Da fadin Manzon Allah ) صلى الله عليه وسلم (ga Aliyyu: "Idan ka fitar da ruwa to ka yi wanka" [Abu Dawud ne ya rawaito shi].


Fitar da ruwa ana nufin fitar maniyyi.


- Mas'aloli..

1- Idan mutum ya yi mafarki amma bai fitar da maniyyi ba, to babu wanka a kanshi, idan kuwa maniyyin ya fito bayan ya farka daga barcin to wajibi ne ya yi wanka.


2- Idan ya ga maniyyi, amma bai iya tuna yaushe ya yi mafarki ba, to wanka ya wajaba a kanshi saboda fitar maniyyin. Manzon Allah ) صلى الله عليه وسلم ( ya ce, "Ana taba ruwa ne saboda fitar ruwa" [Muslim ne ya rawaito shi] Ma'ana ana yin wanka ne don fitar maniyyi.


3- Idan ya ji alamar zuwan maniyyi daga gabansa, amma bai fito ba, to babu wanka a kanshi.


4- Idan maniyyi ya fito saboda wani dalili ko rashin lafiya ba tare da sha'awa ba, to babu wanka a kanshi.


5- Idan mutum yana janaba ya yi wanka, sai kuma maniyyi ya fito bayan ya gama wankan, to ba sai ya sake wankan ba, saboda yawanci yakan fito ne ba tare da sha'awa ba, amma abin da ya fi ya yi alwala.


6- Idan mai barci ya farka, ya ji danshi a jikinsa, amma bai san dalilin zuwanta ba, to dayan abu uku ne :


A) Ya tabbatar da wannan danshin maniyyi ne, to wanka ya tabbata a gareshi, ya tuna ya yi mafarki ko bai tuna ba.

B) Ya tabbatar wannan danshin ba maniyyi ba ne, to wankan Janaba bai wajaba a kanshi ba, hukuncinsa hukuncin fitsari ne, sai ya wanke)

C) Ya yi shakka, maniyyi ne ko ba shi ba ne? To a nan wajibi ne a kanshi ya yi kirdado, idan ya tuna abin da zai nuna masa cewa wannan danshin maniyyi ne, to ya bar shi a kan maniyyi ne, in kuma ya tuna abin da zai nuna masa cewa maziyyi ne, to maziyyin ne, in kuma ya kasa tuna komai, to sai ya yi wanka don fita daga sabani da rudu.


7- Idan ya ga maniyyi, amma bai tuna yaushe ya yi mafarkinsa ba, to wanka ya wajaba a kanshi, ya kuma sake dukkan sallar da ya yi bayan tashinsa daga barcinsa na karshe.


2- Saduwa (Jima'i) Shi ne haduwar gaban namiji da na mace, wato shigar kan gaban namiji gabadayansa cikin farjin mace, ko da kuwa bai zubar da maniyyi ba, saboda fadin Manzon Allah ) صلى الله عليه وسلم ( "Idan kaciyar (namiji) ta shige kaciyar (Mace) to wanka Janaba ya wajaba" [Tirmizi ne ya rawaito shi].


3- Musuluntar Kafiri Saboda "Manzon Allah ) صلى الله عليه وسلم (yaumarci Qaisu dan Asim ya yi wanka lokacin da ya musulunta" [Abu Dawud ne ya rawaito shi]


4- Daukewar Jinin Haila Da Na Biki saboda hadisin Aisha cewa Manzon Allah ) صلى الله عليه وسلم ( ya cewa Fadimatu 'yar Abi Hubaish "Idan al'adarki ta zo, ki bar sallah, idan ya wuce ki yi wankan tsarki ki yi sallah" [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi]. Hukuncin jinin biki kamar hukuncin jinin haila ne da ijma'in malamai.


5- Mutuwa ( صلى الله عليه وسلم ) Saboda fadin Manzon Allah hadisin wanke 'yarsa Zainab lokacin da ta rasu ya ce,"Ku wanketa sau uku, ko sau biyar, ko fiye da haka, in kun ga akwai bukatar hakan" [ Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi].


Wannan Sune abubuwan dake sa wankan janaba ga maza da mata, da fatan kun ilimantu daga abubuwan da kuka Karanta.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post