Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Miji Da Mata |
Yau wannan darasi na masu aure ne, domin nasan da yawa a cikin ma'aurata sun san yadda suka motsa sha'awar junansu. Sai dai kuma akwai wasu hanyoyin da ba sai an kai ga taba juna ba ake iya gane sha'awa ta motsa.
Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Miji Da Mata
Abubuwan da ke tsokano sha'awa tsakanin mace da namiji suna da yawa, amma ga wasu daga cikin su:
1) kallo: Idan namiji yayi duba izuwa mace sai sha'awarsa ta motsa a haka ita ma idan ta dube shi. shi ya sa Allah ya hana muminai maza duba zuwa mtan da ba nasu ba, ya kuma hana muminai mata duba zuwa mazan da ba nasu ba.
Sannan ya kara da cewa: "fadawa muminai maza su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjinsu, wannan shi yafı tsarkaka a Garesu, domin hakika Allah masani ne akan abin da suke aikatawa".
Wannan ita ce dokar da Allah Madaukakin Sarki ya kafawa muminai maza, sannan muminai mata Allah (SAW) ya kafa musu dokoki.
"Gayawa muminai mata su runtse idanuwansu kuma su kiyaye farjinsu kuma kada su bayyana adonsu sai wanda ya bayyana daga garesu, kuma su buga lullubinsu akan kafafunsu kuma kada su bayyana adonsu sai ga mazajensu.
2) Tunani: Idan namiji ko mace suka yi tunani a kan junansu sai sha'awarsu ta motsa. Wata macen idan ta yi tunani kan namiji sai kaga pant din su ya jike, haka shima wani namijin tunanin mace yana sa ya yi inzali.
3) Kwalliya: Kwalliya ita ma tana motsa sha'awar jima'in namiji idan ya ga mace tayi ko ita macen ta ga namiji yayi sai sha'awarsu ta motsa. Shiyasa akeso ma'aurata su dinga yin kwalliya kafin kwanciyar aure.
4) Murya: Muryar mace na ta da sha'awar da namiji idan ya ji muryar mace na zaki sai sha'awar jima'insa ta motsa ko aka kebance mace to da zarar ya ji muryarta sai bukatarsa ta biya. Shi ya sa ma, Manzon Allah (SAW) ya hana mata masu imani bayyana da muryarsu ko da a cikin gidane.
5) Turare: Sanya turare mai kamshi: Yana motsar da sha'awar jima'i ga wanda ya shakeshi. Shiyasa ake son ma'aurata su dinga amfani da turare lokacin da suke son yin kwanciyar jima’i da junansu.
Manzon Allah (SAW) ya ce: Duk matar da ta sa turare ba ga mai gidanta ba, to ba za'a karbi sallartaba har sai ta wanke daga kamshinta. Shi ya sa Manzon Allah (SAW) ya hana mata saka turare idan ba ga mazajensuba.
Shawarwari Kan Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Miji Da Mata
Ki kasance mai kula da wasu manyan gabbai a jikinki domin Manzon Allah (SAW) ya gayawa maza cewa idan kaga wata mace ta burgeshi a waje to ya koma gida gurin tashi abin da ka ga wannan da shi shi ne ga taka, idan kika duba ba wadda tafi wata sai wadda ta fi gyara da kulawa, sai ki ga mutum ya tafi wajen wadda ta fi matarsa shekaru saboda kulawa da goge goge da gyara da dakawa jikinta ba kuma tafı matarsa ba ne amma saboda tanada abubuwan da suke saurin motsa masa sha'awa.
Sai ki kula da gabar farko shi ne:
- Farji : Domin Allah ya kallawafa namiji son sa, don da akwai masu yin aure dan farji kinga lalacewarsa kamar lalacewar auran kine. Domin an ce duk jima'i farjin mace yana fadi da gani daya daga cikin gani dubu shi kuma namiji yana raguwa da gani daya cikin dubu to kin ga ke kina kara girma shi kuma yana raguwa to zai ji yana son karamar yarinya, na hore ki da ki kula da wannan bangaren.
Shawara Ta Biyu Kan Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Miji Da Mata
Ki kasance mai kula da nonuwanki, ita ce babbar gaba ta biyu wacce namiji ke kwallafa rai a kanta kuma tana motsa sha'awar namiji, ki zamo mai boyeshi kar ki dinga barinsa a bude ko'ina yana gani. Domin nono na daga cikin abubuwan dake mosta sha'awar namiji.
Shawara Ta 3 Kan Abubuwan Dake Motsa Sha'awar Miji Da Mata
Kar ki bari sha'awarki ta dauke, idan ta dauke za ki daina bawa mijinki kulawar da ta dace.
Abubuwan dake dauke sha'awa sune
Akwai wata tsoka a jikin farjin mace mai suna bazadaure wadda jinin haila yake bi ta jikinta barin ta tayi dauda yana dauke sha'awa gwargwadon daudarta gwagwadon kwanciyar sha'awarki, idan kuma babu dauda a jikinta to mace zata sami sha'awa sosai.
Abubuwan da ke kawo dauda:-
- Basir.
- Tsoro ko alhini.
- Zazzafan tunani.
- Mace ta rika biyawa kanta bukata, istimna'i
Yin amfani da magunguna marasa inganci wanda ake sakawa a farji. Kada kuma ki bari wani abu ya same ki.
Kangewar sha'awa:- Shi ne mace ta ji bata sha'awar mijinta amma in ta ga wani sai ta ji tana sha'awarsa ko in taji mijinta baya nan amma daga ya dawo sai sha'awarta ta dauke ko idan suka sadu ta ji ba wani gamshashshn dadi. Wannan matasalar idan tana damun namiji ko mace to ana dangantatata da aljanu sai ki rika amfani da dawa'us-sabuni domin yana kona aljani sosai.
Ko sanyi yana daukewa mata sha'awarsu kuma yana hana su haihuwa
Alamun sanyi mai dauke sha'awa
- Fitar farin ruwa ta gaba.
- Warin farji
- Dadewar farji
- Atishawar farji
- Murar farji
- Tsutsar farji
- Lalacewar farji
Fa'idar mujallabul khairi, madfa'ush-sharri da dawa'us- sabuni.
Cututtukan Al'aurar Mata Dake Hana Mace Sha'awa
Bincike ya tabbatar da akwai wasu cututtuka wadanda suke damun al'aurar mata tun daga farkon balagarsu zuwa fara daukar cikinsu da kuma daina al'ada sun hada da:-
- Warin gaba (odur)
- Zafın gaba (pain)
- Kumburin gaba (Inflammatory)
- Zubar ruwa (Leaking)
- Rashin haihuwa (Infertility)
- Sanyi ko zafın mahaifa.
- Kaikayin gaba (Emertic).
Wadannan sune mafi yawan cutattukan al'aurar mata.
Matsalolin Jima'i, Hakika yawaita yin jima'i yana da matsaloli, matsalolin jima'i su ne:-
- Tsoron Jima'i.
- Cutar cikin farji.
- Yana raunana gani.
Mazan da basu da sha'awar Jima'i.
- Yana gadar da ciwon kai.
- Yana raunana jiki rage karfi.
- Yana sa ciwon baya.
Wadannan su ne matsalolin jima'i idan aka yawaita yinsa.
Cututtukan Al'aurar Maza Dake Hanasu Sha'awa, Akwai wasu alamomi wadanda jinsu yana nuni da alamar kamuwa da cutar al'aura.
- Zafın kirji (chest pain).
- Juyawar ciki (Stomach upset).
- Jin kamar zakai amai (Dizziness and nausea).
- Numfashi da kyar (Difficult breathing).
- Naman jiki ya rika zafı kamar wuta (Hot flesh or chills). Karkarwar jiki kamar wani tsoho (Trembling and shaking).
- Jin kamar ana fizgar naman jikinka.
Wannan su ne alamar cutar al'aurar namiji wato (Penis Disease) sai yayi kokarin neman magani. Muna fatan kun gamsu da bayani akan dake motsa sha'awar miji da mata, da kuma matsalolin su.