Abubuwan da muke yi don soyayya |
Abubuwan da muke yi don soyayya" Mata 'yar kasuwa ta yi wa mijinta semo yayin karbar drip.
Abubuwan da muke yi don soyayya, Mata Ta Tuƙawa Mijinta tuwo tana tsaka da karɓar magani
Hotunan wata mata dake fama da rashin lafiya ana tsaka da yi mata ƙarin ruwa ta shiga kicin ta Tuƙawa mijinta tuwo, lamarin ya ja hankalin mutane inda suke ta bayyana ra'ayin su.
Matar mai suna Eniol Fagbemi Sisialagbo ta wallafa a shafinta cewa ta yi fama da zazzabi amma hakan bai hanata hidimtawa mijinta ba. Ga abinda ta rubuta a shafin ta kamar haka;
"Jiya na yi fama da zazzabin cizon sauro, wata kila gudunmuwar jini ya sa na ji rauni a karon farko, ina gida tare da yara sai na kira wata ma’aikaciyar jinya don ta duba lafiyata domin na ji rauni.
Tayi min drip da allura, amma bana son mijina ya dawo gida ba cin abincin dare ba, da kyar na shiga kicin na juya semo ga hubbi, na Kusa gama shirya abinci, hubby ya shigo kicin ya daka min tsawa kan meyasa ba zan zauna na huta don kula da lafiya na ba."
Na ce masa kada ya damu da haka, abubuwan da nake yi ne don soyayya.