Abubuwan Da Kesa Ma’aurata Nisantar Jima’i

Abubuwan Da Kesa Ma’aurata Nisantar Jima’i
Abubuwan Da Kesa Ma’aurata Nisantar Jima’i


Akwai dalilai masu tarin yawa dake saka ma’aurata su nisanci jima’i suji kwata kwata basa sha’awar yin jima’i da junansu.


Kamar yadda bincike ya tabbatar abubuwa da dama suna haddasa rashin samun nishadi da jindadin Jima'i wanda har hakan ke sa ma'aurata su ji basa son kusantar junansu. 


Ga kadan daga cikin dalilan da kesa Ma’aurata su nisanci jima’i kamar haka:


A lokacin da daya daga cikin ma’auratan yadaina tsaftace jikinsa ya zama suna jima’a ne da kazanta. Jima'i baya yin dadi idan babu tsafta tsakanin ma'aurata ko daya daga ciki baida tsafta, misali warin hammata, warin baki, tsamin kai da sauransu. 


A yayinda namiji ya maida matarsa kamar riga ya saka lokacin da yaga dama yacire idan yaso, wato, zaikusanci matarsa banuna kauna da soyayya ballantana wasanni kafin mu’amala. Jima'i baya dadi musamman idanu babu wasanni ko nuna soyayya kafin a fara. 


A yayinda namiji ya daina damuwa da karfin gabansa ya zama mintuna kadan yagama biyan bukatarsa. Mata basa son haka irin wannan dalilin ne ke sa mace taji bata kaunar yin Jima'i gabaki daya. 


A yayinda mace tadena aske muhimman gurare ajikinta kokuma tabarsu cikin datti suyi ta wari.


A yayin da ma’aurata suka kasa fahimtar irin nau’in kwanciyar da tafi gamsar da junansu, domin wata kwanciyar na cutar da dayansu.


A lokacin da nammiji ko matar ke fama da warin baki da na jiki da hammata. Dole ne a yi kokarin tsafta ce jiki kafin a fara Jima'i. Tsafta na daga abinda ke kara dandano da dadin jima'i. 


Yayinda ma’aurata suka kasa samarwa junansu lokacin da yadace da yin jima’i, samun lokacin yin Jima'i da ya dace na taimakawa wajen inganta dadin jima'i tsakanin ma'aurata. 


Yayinda ma’aurata ya zama kullum salon yin jima’insu iri daya ne kuma a guri guda, sannan kuma basa nunawa juna jindadinsu da juna a lokacin da daya daga cikinsu ke cikin damuwa ko wata matsala.


Yayinda Kuke da matsalolin infection (ciwon sanyi). Wannan yana daga cikin abinda ke jawo rashin samun jindadin Jima'i tsakanin ma'aurata. Dole a yi kokarin magance matsalar infection. 


Zama da kayan da basu dace ba a lokacin da yakamata ace an kusanci juna. A Yi kokarin yin saka kayan da suka dace kafin Jima'i. 


Sakarwa miji ragamar komai sai yanda yajuyaki Kusan da cewa ana samun kiyayya a tsakanin ma’aurata yayin jima’i. Hakika akwai dabi’u da wasu keyi yayin jima’i irin wadannan halayen na jawo kiyayya ta a tsakanin ma’aurata rana tsaka miji zaiji kinfita daga ransa kokuma ke kiji haka batare da wani laifin da kuka yiwa juna ba. 


Kuma dadama hakan tana faruwa rana tsaka ma’aurata su daina kusantar juna babu dalili.


Wannan Sune abubuwan dake sa ma'aurata nisantar Jima'i da junansu. Da fatan za'a kula tare da magance matsalolin dake jawo ko haddasa rashin samun jindadin Jima'i.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post