Abubuwan Da Ke Jawo Rashin Haihuwa Ga Namiji

Abubuwan Da Ke Jawo Rashin Haihuwa Ga Namiji
Abubuwan Da Ke Jawo Rashin Haihuwa Ga  Namiji 


Abubuwan Da Ke Jawo Rashin Haihuwa Ga  Namiji 


Akwai mazan da basa haihuwa a dalilin rashin lafiya ko kuma halitta daga Allah (S.W.T). Kasaka mace tasamu juna biyu yazama wajibi abi wadannan hanyoyin;


1) Samar da lafiyayyen maniyyi wanda wannan yana bayuwa ne ta bangaren girma da kuma samuwar halittar namiji bangaren haihuwa yayin balagar shi, wanda yazama wajibi ya zamto cewa marena namiji ko daya daga ciki yanada cikakkiyar lafiyar samar da sinadarin testesterone da kuma sauran sinadaren da zasu taimaka wajen samuwar ingantaccen maniyyi

2) Yazama wajibi a dauki maniyyi cikin bututun daukar maniyyi bayan samuwar shi a hada shi da abinda ake cema semen. Yayinda mutum zai inzali maniyyi zai fita daga marena cikin wani bututu sai ayi mix din shi semen sai a fitar dashi ta kofar zakari yayin inzali

3) karancin ruwan maniyyi kasada 15 millions per mill of sperm ko kuma kasa da 39 million of sperm count ga duka abunda ya fita bayan inzali

4) Idan tafiyar maniyyin mutum yasamu tangarda(sperm motility) yana gaza kaiwa ga kwan mace har kuma ya barbare shi ko kuma ya shige shi.


Rashin Lafiyar Da Ke Iya Saka Rashin Haihuwa Ga Da Namiji 

1) Varicocele, kumburewar jijiyoyin dake maida jini ga zuciya daga marena wanda wannan yana saka karancin samuwar maniyyi ko kuma rashin nagartar maniyin

2) Infection, Cutar da kwayoyin halitta wato microbes ke sawa ga jiki misalin kumburin marena ko epydydimitis tana saka tabo wanda tabon ka iya sa dadewar bututun daukar maniyyi wanda zai fitar dashi ta kofar zakari namiji zuwa ga farjin mace, irin su gonorrhoe HIV da sauran cututtukan da akan iya dauka ta hanyar saduwa na iya saka lalacewar marena ta har abada.

3) Matsalar inzali, kamar wadanda maniyyin su ke shiga cikin bladder akasin fita ta kan zakarin su yayin inzali (retrogade ejaculation). Cutuka kamar ciwon sugar, cutar lakka ko raunin lakka ko kuma yin aikin tiyata ga prostate, bladder ko sandar mafitsara duk suna kawo hakan

4) kwayoyin halitta masu yakar cututtukan jiki na iya yakar maniyyi su kashe shi

5) Cancer da waninta na iya takura guraren da suke samar da sinadarin haihuwa

6) Tsayawar marena a cikin ciki ba cikin jikkar marena ba lokacin girman jikin mutun daga yarinta zuwa balaga

7) Rashin wadatar sinadarin hormones na da namiji ko kuma wucewar yawan su daga daidai

8) matsala ta bangaren saduwa, kamar rashin karfin mazakuta, saurin inzali kafin gamsar da mace ko kuma kofar azzakari kasan shi ba ga kanshi ba


Matsalolin Wurin Zama Wadanda Ke Hana Haihuwa Ga Da Namiji 

1) Sinadaran gubar masana'antu gubar kashe kwari, gubar kashe haki, gubar yin fenti suna bada gudummuwa wajen karancin maniyyi

2) yawan yin hoton xray yana saka rashin haihuwa ga da namiji

3) saka kayan da zasu matse ka ko kuma abunda zai saka maka zafi ga marena na tsawon lokaci nasa karancin ruwan maniyyi

4) magunguna misali shan maganin da zai sa ginuwa da karfin tsokokin jiki na saka marena su tamuke a samu karancin maniyyi

5) Shan giya na kawo raguwar sinadarin testesterone wanda yana rage karfin mazakunta a samu karancin maniyyi, sannan cutar hanta nada nasaba da hana haihuwa

6) Kiba, tana saka karancin maniyyi ko ta saka tangarda ga sinadarin hormone na haihuwa gun da namiji.


Lokacin Da Ya Kamata Kaga Likita 

Da zarar kanada alamomi kamar haka ;

1) Rashin karfin mazakunta ko kuma saurin inzali yayin saduwa da Iyali, rashin wadataccen maniyyi ko rashin ingantaccen maniyyi

2) Rashin sha'awar diya mace ko qarancin son yin jima''i da mace

3) Jin ciwo kumburi, ko kuma cancer ga wajen marena

4) Idan abokiyar zamanka ta wuce shekaru 35

5) Idan kana da tarihin tiyatar aiki ga marena, ko prostate ko kuma matsalar saduwa da iyali

6) Ko anyimaka tiyatar aiki ga marena, ko prostate ko azzakari.

                     

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post