Abubuwan Da Ke Iya Jawo Barin Ciki Ko Zubewar Ciki

Abubuwan Da Ke Iya Jawo Barin Ciki Ko Zubewar Ciki

 Barin Ciki Ko Zubewar Ciki 


Abubuwan Da Ke Iya Jawo Barin Ciki Ko Zubewar Ciki 


- Matsala a halittar jariri (sanin abinda ke

janyo wannan sai Allah)

- matsanancin infection

- rashin lafiyan da ke sanya matsanancin

zazzaɓi

- shan magani ba bisa ka'ida ba ( maganin

turawa ko na gargajiya)

- rashin isasshen garkuwar jiki a mace mai ciki

- karancin jini ko matsalolin jini

- ciwon suga

- hawan jini

- matsalar mahaifa ko bakin mahaifa

- matsalar sinadaran da thyroid ke fitarwa.

(Thyroid halitta ce da ke da wiyan ɗan adam. Tana na da amfani sosai)

- shan sigari

- yawan shan Nescafe ko coffee


Alamomin Bari Ko Zubewar Ciki 

- Fitar wasu ruwa daga gaban mce
- zubda jini
- fitar wani abu kamar tsoka tsoka ko Nama
- matsanancin ciwon mara
- matsanancin ciwon baya wanda ya fara
kwatsam lokaci guda
- yawan shekaru ga mace. Ma'ana mace da ta
fara manyan ta.

Idan mace ta samu barin ciki ya na yiwuwa duk abin da ke cikin ya fito ga ba ki daya ko kuma wani abu ya saura. Idan wani bangaren cikin yai saura a cikin mace dole ne a dauki mataki a asibiti.

Wankin mara da ake yi a asibiti bayan mace ta yi bari ba ya da matsala ko kaɗan. Hasali ma ya na taimakawa jinin ya tsaya. Kuma ya na taimakawa domin mace ta iya sake ɗaukar wani ciki bayan ta warke.


Bari Ko Zubewar Ciki Kala Kala Ne akwai:

Threatened abortion, ma'ana cikin da ke nuna alamun zubewa
Inevitable abortion, ma'ana cikin da likitoci sun duba kuma sun auna Kuma sun gano babu makawa sai cikin ya zube
Complete abortion, ma'ana cikin da ya zube
gaba ki daya kuma babu abin da ya saura a
cikin.
Incomplete abortion, ma'ana cikin da ya Zube amma akwai abin da ya rage a cikin ciki. (Aasibiti kaɗai za a iya gano wannan kuma a ɗauki matakin da ya dace)

Idan mace ta yi bari a asibiti ne za a gano
matakin da ya dace a ɗaukar. Mace da tayi bari ya na da kyau ta sani cewa ba gazawa ne daga gareta ba, abu ne wanda ya na
iya faruwa ko da mace ta bi shawararin da aka bata a asibiti. Allah Ya sauke duk masu ciki lafiya.

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post