Abubuwa 7 Dake Jawo Mai juna Biyu Tai Barin Cikin Ko Ya Zube - Android Pols

Abubuwa 7 Dake Jawo Mai juna Biyu Tai Barin Cikin Ko Ya Zube
Abubuwa 7 Dake Jawo Mai juna Biyu Tai Barin Cikin Ko Ya Zube  


Ya ya mace ko ma'aurata za su gane ko su fahimci ciki ya Zube ko ya lalace idan basu kula da abubuwa 7 ba. 


Magidanta za su fahimci lallai sun samu karuwa ta ciki bayan dakatawar al'adar na wani lokaci, idan mace ta fahimci lokacin al'adar ta ya shige bata ga jini ba yana daga cikin alamun farko da zata fahimci ta dauki ciki.

A daidai wannan lokacin wajibinta ne ta tabbatar da cikin ko akasin hakan ta hanyar yin awo. Idan akai awo aka tabbatar da akwai ciki to akwai hanyoyin da suka dace a dora mace ko tayi amfani da wasu mahimman shawarwari dan renon cikin.

Akwai wasu matsalolin da suke saurin zubar da cikin da baiyi kwari ba daga cikin su zan zayyano kadan. Duk matar da ta ke da cikin da bai wuce wata 3 ba to takula da wadannan matsalolin kamar haka.


Abubuwa 7 Dake Jawo Barin ciki ko zubewar juna Biyu

1- Malaria, wajibin mace ne ta kula da hanyoyin kare Kai daga kamuwa da zazzabin Malaria, cikin lokaci malaria na lalata cikin diya mace. Da zarar kin ji sauyin yanayi ko yawan zazzabi dai ki tinkari likita. 

2- Hawan jini, daga lokacin da mace ta samu ciki, maigida ya tabbatar da jinin uwar gida bai rika hawa ba, duk wata hanya da jinin ta zai rika hawa a magance su daga ciki hadda labarta mata za ai mata kishiya.

3- Tsananta Mata, Yawan kusantar ta ko matsin lamba a bangaren saduwa na taka mahimmiyar rawa wajen lalata ciki wanda Bai dadeba.

4- Aiki Mai tsanani, Yana daga cikin tausayi daga magidanta su takaita wa matansu masu ciki su aiki mai yawa daga lokacin da cikin su Yana karami, da rage tafiye tafiye.

5- Anfani da ingantaccen abinci Mai Gina jiki, lallai ya kamata mu rubanya abincin da muke samar wa matanmu, mai kyau, mai dadi da Kuma jan lokaci, sannnan duk abunda mace tafi bukata a bayar da muhimmanci akansa  matukar zai amfanar da ita.

6- Tsafta, sai mun rufe Ido mun kula da tsaftar muhallin gidajenmu, da dama Mata na samun rauni da zaran sun dauki ciki sai kaga mace tsaftar ta ragu.

7- Matayenmu su zama Yan lelenmu, wasu mazan na dabi'ar banza da zaran matan su sun samu ciki maimakon su samu kula fiye da baya sai kaga ana jin haushi da kyamar su, to wajibinmu mune mu tausaya masu, mu Samar masu da kayan dadi.

Wadannan sune abubuwa 7 dake jawo mata masu juna biyu su yi barin ciki ko zubewar ciki. Da fatan maigidanta za su kula sosai akan matansu dake da juna biyu wajen samar musu da kayan abinci masu gina jiki da kara musu lafiya. Sannan su rage yawan yin ayyukan wahala da suka saba yi a baya.

 

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post