Abincin dake sa kiba |
Abubuwan da mutum zai dinga ci Idan yanaso Kara kiba
Mutane da yawa na son rage kiba a yayin da wasu kuma ke son su Kara kiba, hakan yasa a yau muka kawo muku nau'in abincin dake sa kiba idan ana cin su cikin karamin lokaci.
Akwai abincin da cin su ke taimakawa wajen Karin kiba da lafiyar jiki, sannan kuma akwai wasu dabi'u da suke taimakawa mutum kara kiba idan ana yin su. Ga su kamar haka;
Abincin dake sa kiba
Mutum yana gama cin abinci ya kwanta ba tare da ya mike tsaye ba ya tattaka ko da taku 20 ne zuwa da dawowa.
Shan damammiyar fura da safe da nono mai kauri Kafın aci komai.
yawan shan alewa chocolate.
yawan shan kayan cocoa a shayi.
cin nama mai kitse.
yawan cin kwai (egg).
cin farar kaza.
yawan shan lemon kwalba ko na kwali ko na gwangwani.
rashin motsa jiki.
Idan kunaso ku kara kiba sai kun kiyaye da ci da kuma yin wadannan abubuwa da muka lissafa a sama. Da fatan ku ilimantu.