Yanda Zaka Tsara Mace Da Kalaman Soyayya A Karin Farko |
Idan kaga 'yar budurwa tana tafiya sai kaga tashiga zuciyarka kuma kanason yi mata magana. Ga wasu daga cikin kalaman so da Zakai amfani dasu
A matsayinka na saurayi ka taba tsayar da budurwa a hanya ka yi mata kalaman soyayya da suka ratsa Jikinta har ta karbi soyayyar ka? Idan baka taba yin hakan ba ko kuma idan kana son sanin sirrin samun yadda kake so ka Karanta wannan topic har zuwa karshe.
Idan kaga 'yar baby tana tafiya sai kaga tashiga zuciyarka kuma kanason yi mata magana. Ga wasu daga cikin kalaman soyayya da za kai amfani dasu don shawo kanta har ta amince da kudurin ka.
(1) Ka tabbata kaima ka hadu, ma'ana ka dau wanka mai kyau saboda wanka yana daya daga cikin abunda ke sato maka zuciyara mace. Sannan kafin ka yi mata magana sai ka tabbata tazo dai dai gurin da babu mutane sosai don wata tana da alkunya ba ko ina zata iya tsayawa ba koda tana so.
(2) Idan ka karasa gurinta da kaje sai kafara yi mata sallama kamar yadda addininmu ya tanadar. Nasan indai ta cika musulma zata amsamaka kaga kasamo hankalinta kenan.
(3) Kalmar so ta farko da za kai mata shine. Sai kace ranki yadade kiyi hakuri fah nasan ba mutuncin kyakkyawar mace mai haiba da asali bane ta tsaya ta kula namiji a yayin da take tafıya izuwa wani guri, amma kiyi hakuri nima bayin kaina bane wani sashen bangaren jikinane ya uzuramin dole sai nayi hakan tun yayin da idanuwana su kai arba da wannan kyakkyawar surar taki.
(4) Kar dai in cikaki da surutu nasan kina sauri ne saboda haka nake neman wata alfarma guda 2 zuwa 3 a gunki. Anan za ka ji ta cema inajinka.
(5) Don Allah menene sunan hajiyar ne? Zata iya fadama gskiya za kuma ta'iya fadama karya idan mai class ce.
(6) Ammm don Allah ko zan iya samun full adress naki? Idan kayi mata a lokacin zata baka dai-dai. Idan baka yi mataba zata baka wrong.
(7) Sai kuma alfarmar karshe wacce tafi kowacce wuya kace don Allah inason kibani phone number naki. Nanma idan kayi mata zata baka idan bakayi mata ba za tace ai bata da phone.
Karka sake tashin farko ka furta kalmar so a gareta, ko wasu zafafan kalaman soyayya, hasalima da kasan takunka sai kaci gaba da sace zuciyarta da mugayen kalamai masu karya garkuwar jiki gami da sace zuciyar mace. Cikin kankanin Iokaci da kanta idan har kayi tasiri a zuciyarta zata furtama kalmar so.
Ina gayamuku wannan ne a Iokacin da har kaje gidansu kun fara sabawa. Kunsan mata dai akwai son kulawa idan kuwa aka samu akasin hakan zaka ga ba daidai ba. Sannan suna da bukatar a rinka yabonsu koda kuwa sun san yabon da kake musu ba su kai matsayin ba. Mata dai akwai son abun dariya yayin da kuka kasance ma'abuta soyyaya. Mata dai suna son shagwaba amma ba ta hauka ba.