Yadda Zaka Iya Gane Mace Ta Kamu Da Son Ka - Android Pols

Yadda Zaka Iya Gane Mace Ta Kamu Da Son Ka

Yadda Zaka Iya Gane Mace Ta Kamu Da Son Ka 


Yadda Zaka Iya Gane Mace Ta Kamu Da Son Ka: Zata riƙa yawan yi maka murmushi akan abubuwan da yin murmushi akan su bai da wani muhimmanci


Kamar yadda zamu iya shaidawa a kusan dukkanin halittun da suke faɗin duniyar nan, zamu ga cewa mazaje sune suke fara ko yunƙurin neman mata. Domin kuwa ba kasafai ake samun mata suna neman maza ba. Idan mace tana son ka baza ta gaya maka da baki ba, amma zata gaya maka da yanayin motsin jikin ta. 

Jikin mutum ya kasance yana fayyace abun dake cikin ran shi ta yanayin yadda mutum yake matsawa, tsayuwa da kuma yanayin fuskar mutum koda kuwa mutum bai yi magana ba. Galibi mata suna nuna wasu alamu ne dake nuna cewa suna son namiji.

Waɗannan alamun suna bayyana sune ba tare da sun ankara ba, idan mace tana son ka ba zai yu ta iya ɓoyewa ba. Hakan kenan yana nufin dole namiji ya zamo mai ƙwarin gwiwar neman mace da soyayya, to kenan mazaje masu kunya baza su iya samun budurwa ba kenan? Zamu bada amsar wannan tambayar a wasu darasin na gaba.

 

Yadda Namiji Zai Gane Mace Na Son Sa 

Ga wasu daga cikin alamomin da suke nuna cewa mace tana son namiji;

1) Zata riƙa neman taga cewa tayi maka magana, misali ta hanyar yi maka wasu tambayoyi akan abubuwan da ta sani.

2) Zata riƙa yawan yi maka murmushi akan abubuwan da yin murmushi akan su bai da wani muhimmanci.

3) Zata riƙa yawan taɓa gashin kai a sa'ilin da take yin magana dakai.

4) Zata riƙa yawan gyaran jikin ta a lokacin da take tare da kai.

5) Zaka riƙa yawan haɗuwa da ita a gurare mabanbanta.

 

Zaka fahimci cewa bata ruɗewa idan tana magana a gaban wasu mazajen, amma kai kuma tana ruɗewa idan tana yin magana da kai, hakan duk alamu ne yadda zaka gane son ka take.

Abun da nake nufi da ruɗewa anan shi ne irin ruɗewa da mutum zai yi misali idan ya shiga ofishin wani babban jami'i kamar dai manajan wani kamfani idan yaje neman aiki, dalilin da yasa mutum yake wannan ruɗewar shine saboda yana ganin wannan mutumin da martaba. To kamar haka ne itama martabar ka da take gani shine zai sa ta ruɗewa idan tana gaban ka.

Ƙwayoyin idanuwan ta zasu wage a lokacin da ta haɗu da kai (amma ka sani wagewan ƙwayoyin idanuwa alama ce kuma na jin tsoro ko fusata). Kuma zaka samu tana juyawa ta fuskance ka.

Wannan sune alamomin na yadda zaka gane mace ko budurwa na son ka. Shin kuna taba samun matan dake yi muku hakan amma baku fuskanci son ka take yi ba? Ku bayyana mana ra'ayoyin ku a kasa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post