Yadda Zaka Ci Ribar Zama Da Mace - Android Pols

Yadda Zaka Ci Ribar Zama Da Mace
Yadda Zaka Ci Ribar Zama Da Mace


Yadda Zaka Ci Ribar Zama Da Mace 


Imamu Ahmad (RA)  ya yi wa dansa wasiyya da wasu abubuwa guda (10) wadanda za su taimaka wajen zama da mace lafiya musamman matar aure.


Yace ya kai ɗa na, haƙiƙa ba zaka taɓa samun jin daɗin zamantakewar aure a cikin gidanka ba har sai ka kiyaye dabi'u (10) da zaka mu'amalanci matarka dasu don haka ka kiyaye su. Ga su kamar haka;


Na Ɗaya Da Na Biyu: 

Haƙiƙa su mata suna son tausaswa da ja ajiki kuma suna son a dinga cewa ana son su ana ƙaunarsu. Don haka kada ka dinga yi musu rowar faɗar haka, idan kuwa ka yi rowar to ka sanya hijabi tsakaninka da ita na samun  Ƙarancin soyayya da ƙauna.


Na Uku: Ka sani cewa su mata ba sa son mutum mai tsanani mai mugun takurawa, idan ka fahimce su, suna yiwa mutum rarrauna hidima. Don haka kowacce sifa ka ajiye ta a gurin da ta dace domin hakan shi zai fi jawo ƙauna  da nutsuwa a tsakaninku


Na Huɗu: Haƙiƙa su ma mata suna son irin abinda namiji ya ke so daga gurin mace, kamar daddaɗan ƙamshi, magana mai daɗi, kyak-kyawar Shiga, tashin kanshi da dai sauransu. To don haka ka sifantu da dukkan waɗannan halaye a dukkan yanayinka.


Na Biyar: Ka sani cewa Gida wata masarauta ce ta mace wadda take jin cikakken iko a cikinta kuma take jin cewa itace shugaba a cikinsa. To ina Jan kunnenka da Kada ka kuskura ka rusa wannan masarauta, kana mai Nuna mata cewa ita ba kowa bace ko kuma gidanka ne sai yadda ka so sai abinda ka so, idan kayi haka to ka tumbuke ta daga kan sarautarta, kuma mai mulki bashi da wani abokin gaba a Duniya fiye da Wanda ya sauke shi daga kan mulkinsa


Na Shida: Dukkan matara aure tana son ta yiwa mijinta hidima amma kuma bata son ta rabu da 'Yan uwanta, kada kayi ƙoƙarin raba ta da danginta ta hanyar bata zabin ko kai ko danginta, domin idan ta Zabe ka akan danginta to babu shakka zaka dawwama cikin bakin ciki da Bacin rai da za ka dinga samu daga gare su.


Na Bakwai: Haƙiƙa ita  mace an halicce ta ne daga ƙashin haƙarƙarin namiji karkatacce, wannan kuma ba aibu bane a gareta shi ne ma kuma sirrin kyawunta da kuma Jan hankalin da take yiwa maza, don haka kada ka hayayyaƙo mata a lokacin da ta yi wani kuskure kana ƙoƙarin gyara ta ta karfin tsiya sai ka Karya ta, karya ta kuwa shine sakinta.


kada kuma ka kyale ta tayi abinda taga dama ko kuma taci gaba da yin kuskuren, da  sunan a karkace take, domin sai ta bijire maka daga karshe taki yi maka biyayya, kai dai ka kasance da ita baina-baina.


Na Takwas:  kuma ka sani cewa su mata sun dabi'antu akan Kafircewa miji da yi masa butulci da kuma musun abin alheri. Idan da zaka kyautatawa mace tsawon shekara ko zamani sai wataran ka munana mata, za ta ce me ka taba yi min?. To kada wannan hali Nata ya sa ka kyamace ta gaba daya, domin idan ka kyamaci wannan dabi'ar daga gare ta to zaka yarda kuma da wasu halayen nata  masu kyau


Na Tara: Ita mace ba kamar Namiji bace, tana rayuwa ne cikin rauni na jiki dana ruhi, saboda haka ne ma Allah (SWT) ya ɗauke mata wasu daga cikin farillan da ya wajabta mata a waɗannan lokuta saboda wannan rauni na ta. Dubi yadda Allah ya ɗauke mata sallah kacokan a wannan yanayi ( na haila) ya jinkirta mata rama azumi har sai lafiyar ta ta dawo nishadinta ya daidaitu, to ka sauƙaƙa mata umarnika da hane-hanenka a wannan yanayi kamar yadda ubangijinta ya sauƙaƙa mata farillansa.


Na Goma: Ka sani cewa ita matar aure ribatacciyar baiwa ce a hannunka, don haka ka ji Kanta ka tausaya mata ka kuma ɗauke kai dangane da rauninta sai ta zamar maka kyak-kyawar abokiyar zama kuma mace ta gari.


Annabi (SAW)  yace" Inai muku wasiyya da mata Ku rike su da alheri, domin ita mace an halicce ta ne daga kashi tanƙwararre kuma Mafi tankwarewar kashi shi ne sama, idan ka matsa sai ka tayar dashi to zaka karya shi, idan kuma ka barshi haka to zai dawwama a tanƙware kuma a karkace,  to don haka inai muku wasiyya ta gari dangane da mata.


Kuma Annabi (SAW) yace" fiyayyenku shi ne fiyayyenku ga iyalansa kuma ni ne mafi alherinku dangane da iyalaina"


Allah ya bamu ikon zama da iyalanmu lafiya Amin.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post