Yadda Za ka daura whatsapp ɗaya a wasu wayoyi da yawa |
Yadda Za ka daura whatsapp ɗaya a wasu wayoyi da yawa
Yau zan yi muku bayani ne kan yadda zaka iya ɗaura Whatsapps ɗaya a wayoyi 2 zuwa adadin yadda kake so. Misali idan kana da kamfani kana son ka ɗaura kamfanin Whatsapps dinka a duk wayoyin da ƴan aikin ka za su ke kula da abubuwan dake faruwa.
Ko kuma iyaye dake son kula da abubuwan da ƴaƴansu ke yi, ko mijin dake son sanin abinda matarsa ke yi a Whatsapps zaka iya yin hakan ta cikin hanya mafi sauƙi.
Da farko dai duk wanda yakeso yai hakan sai ya bi waɗannan hanyoyi da za mu bayyana muku su. Sannan kuma za ku iya kallon wannan VIDEO don ganin yadda ake yi.
Yadda Ake ka daura whatsapp ɗaya a wasu wayoyi Fiye Da Biyu
- Da farko za ka shiga play store ka fara yin update na Whatsapps dinka .
- Daidai inda zaka yi register number wayarka daga sama hannun dama zakaga wasu madannai 3 a ɓangaren dama sai ku taɓa.
- Idan ka danna waɗannan madannai za kaga an rubuta Link Device, sai ka taɓa za kaga Camera scanin zai nuna maka yadda zaka ɗauki hoton wayar da kake so ka dinga ganin chat din su.
kuna iya kallon wannan VIDEO don ku ga bayani da misalai dalla-dalla na yadda ake iya ɗora Whatsapps ɗaya a wayoyi sama da biyu.
Moustapha
ReplyDelete