Yadda Samari Za Su Ƙauracewa Auren Sha'awa Su Yi Dace Da Matar Aure Ta Gari |
Matakai 5 da matasa za su bi don samun auren mace Tagari
Kowa da irin macen da yake son aura, munyi nazari kan auren sha'awa da matasa keyi a wannan zamanin da kuma matakai 5 na yadda samari za su zabi mace tagari.
Babu shakka kowani namiji yana da kalar macen da yake son ya aura wani yana son ya auren baƙar mace yayin da wani kuma yana son ya auri fara, wani kuma so yake ya auri mace ƴar masu kuɗi.
To Ba anan take ba, bayan zaɓin kalar macen aure, akasarin maza suna siffanta siffofin macen da yake son ya aura, wani yana son mace mai kwankwaso(hip) yayin da wani zai ce maka shifa yana son mace kamar coca-cola tsakiya siririya, daidai duwawun ta kuma, su zama masu faɗi, yayin da ƙirjin ta kuma ya zama ya cika, wannan duk kalamai ne na maza da suke son mace a tsarin irin na sha'awa, ba wai halayya ta zamantakewa ba.
Matakai 5 Don Zabar Mace Ta Gari
A duk lokacin da matasa suke ƙokarin shiga cikin rayuwar soyayya ta aure, to kada su manta da wasu abubuwa guda biyar 5, waɗanda zasu taimaka musu wajen zaɓen mace da ta dace da su. Wasu masana halayyan ɗan adam sun bayyanar da wasu abubuwa biyar da duk na miji ko mace suka ɗauke su, babu shakka baza suyi kunya ba a rayuwar aure.
- Kafin ka zurfafa cikin kogin soyayya da mace, yana da kyau kasan wane irin tarbiyya iyayen ta suka bata, musanman mahaifi, irin ‘yayan nan ne da ake shagwabawa? Ko kuwa irin yaran da basu da kamun kai ne suna iya tambayar saurayi wani abu tun kafin aure?
- A duk lokacin da kake ƙoƙarin kiran mace amma tana yawan yi maka kukan cewar ta gaji, koda kuwa bata yi wani aiki da ya kamata ace ta gaji ba, ko kuma ka fuskanci cewar bata son duk wani aikin motsa jiki, ta cika son kanta. To kaji tsoron son auren irin su.
- Mace ce mai tausayi ko kuwa irin zubin matane da basu da damuwar halin da mutun ya shiga. A wasu lokaci yana da kyau ka gwada ta da wani abu don ganin yadda zata dubi abun, idan ta nuna tausayi da damuwa to lallai sai ka ƙara gyara dangantar ku.
- Hakama duk mace da ka lura tana da alamun rashin gaskiya a tare da ita, dangane da tarayyar ku, to itama ba mace da ta dace mutun ya nema da aure bace. Gaskiya da mutunta juna shine babban ginshiki a duk rayuwar zamantakewar aure.
- Ka tabbatar da Macen da kake son aura mai ilimi ce musamman ilmin addini, domin kuwa idan ka auri mace mara ilimi bakai sa'ar aure ba. Kada kyau ko kuɗi ya ruɗe ka domin kuwa zakai nadama.
Waɗannan sune abubuwa 5 da ya dace duk matasa su yi la'akari dasu a yayin neman matan aure, samun mace tagari a rayuwar aure shine babban burin duk wani namiji nagari. Allah ya haɗa kowa da rabonsa na alheri amin.