jarumar Kannywood Fati Ladan tayi bikin cika shekara 10 da aure |
Tsohuwar jaruma a masana'antar Kannywood Fati Ladan ta cika shekara 10 da aure
A ranar Laraba, 20 ga Disamba, 2023 tsohuwar jarumar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, da mijin ta, Alhaji Yerima Shettima, su ka cika shekara 10 da aure.
Domin yi wa Allah godiya da ya nuna masu wannan lokaci, an yi saukar Alƙur’ani a safiyar Alhamis a gidan su da ke Yarima Close a cikin rukunin gidajen Jinya Close da ke Titin Kanta a cikin garin Kaduna.
Fati da Yerima |
Tun da farko an fara gudanar da addu’o’i ga ma’auratan da kuma ƙasa baki ɗaya. Daga nan alarammomi su ka fara karatu bisa umarnin jagoran su. Inda aka kammala saukar Alƙur’anin da misalin ƙarfe 10:40, sannan aka ƙara yin addu’o’in ƙarin zaman lafiya ga Fati da Yerima. Bayan an gama, sai aka fito da abinci da abin sha, aka yi walima, kamar yadda shafin Film Magazine ya rawaito.
Da misalin ƙarfe 2:30 na rana, an yi ƙasaitacciyar walima ta ‘yan’uwa, ƙawaye, abokai da abokan arziki. Duk da cewa ba kowa aka gayyata ba, amma taron ya samu halartar ɗimbin mutane daga wurare daban-daban. An ci, an sha.
Bayan kammala ciye-ciye da tanɗe-tanɗe, sai ma’auratan su ka yanka kek don nuna farin cikin su da Allah ya nuna masu wannan rana. Yerima da Fati sun ba junan su kek ɗin da su ka yanka a baki.
Fati da Yerima |
‘Yan’uwa da abokan arziki sun taya su murna tare da yi masu addu’ar ƙara danƙon so da ƙaunar. An tashi daga wajen taron da misalin ƙarfe 5:30 na yamma.
‘Yan Kannywood su ka halarci walimar sun haɗa da Abbas Sadiq, Jamilu Adamu Kochila, Zaharaddin Mando, Al-Amin Abdullahi Albani da Wasila Isma’il.
Allah ya ƙara masu zaman lafiya da danƙon soyayya.