Yadda Ake Zaman Aure Da Namiji Mai Saurin Fushi |
Yadda Ake Zaman Aure Da Namiji Mai Saurin Fushi: Idan mace ta auri namiji mai saurin fushi tana cikin matsala
kowane mutum yana fushi akwai sinadaran fushi acikin kwakwalai da suke a tara wanda dan adam ke gadosu daga iyayen sa. Idan kasan kanada sanadaran da yawa sai ka zama mai saurin fushi.
Idan mace ta auri namiji mai saurin fushi tana cikin matsala, kuma idan ba ta bi a hankali ba watarana akan abu kadan zai yi mata duka ya farfasa mata jiki har da karya hakori, wani lokacin ma har da karya kafa.
Yar uwa idan kina da namiji me yawan fushi to ana so ki zama mai lura sosai da wadannan abubuwa:
Menene yake saurin sauko dashi idan yayi fushi?
Wani namijin baya son yawan surutu in yana jin yunwa, ko idan yadawo daga gun aiki.
Wani namijinn yakan ji saurin fushi in bashi da kudi ko yaje sana'arsa bai samo komaiba.
Wani kuma yafi fushi da bata rai idan ya samu kudi ko ya dauki albashi duk dan karki dameshi da kinmatsa kuwa za a bata.
Wani idan aka batamasa rai a waje koda a musune sai ya dawo gida da fushi, da zarar kin tsokanoshi kadan sai ki taka sawun barawa yai tai miki masifa idan ba kiyi sa'a ba zai iya yi miki duka.
Wani baya so yanai miki magana kema kinai masa magana sai yai fushi da harzuka, zai ga kinma raina shi yana magana kina magana ya fi son idan ya fada kiyi shuru har sai ya gama.
Wani namijin kuma hakan ya tsana, yafi son yana fada kina fada, idan kuma kin yi shiru sai ya dauka kin raina shine.
Wani kuma baya son gatse ko zolaya ko yawan wasa, nan da nan sai ya hau fushi.
Dan haka ke zaki karanci halin mijinki kisan yadda yake da kuma hanyoyin da zakina mu amalantarsa.
Sannan kuma dole ne ki zama mai hakuri fiye da kowace mace, amma idan ba haka ba gidanki zai zama tamkar fagen wajen fada, sai kiga kun fita daban a unguwa, yaranku haka za su taso.
Tayaya Za'a Canja Dabi'ar Saurin Fushi ?
Aiki da ilmi da tarbiyyar muslunci sune kadai zasu saita mutum me yawan fushi domin akan sami me tarin ilmi amma baya aiki da ilimin, sai kaga da ransa ya baci ya tabka wani rashin da'ar.
Amma duk me aiki da ilminsa da ransa yabaci yayi fushi to zai nemi taimakon Allah sai kuga yaki yanke hukunci cikin fushi kamar yadda Manzon rahama (S.A.W) ya umarta.
Domin shi fushi dabi'a ce a jikin rai baka da ikon hana kanka jinsa amma sai annabin Rahama yace ka zama mai mallakar zuciyarka a yayin fushi, ya kuma hanaka yanke hukunci a yayin fushi.
Da fatan maza masu saurin fushi da matansu za su kula kuma su rage. Kuma su gane raunin dake tattare da su na hankali tunani hali da da kuma jiki.