Yadda Ake Yin Wankan Tsarki A Bisa Koyarwar Ahlul-bait (AS) |
Yadda Ake Yin Wankan Tsarki A Bisa Koyarwar Ahlul-bait (AS).
Ga Bayani A Takaice Dangane da Wankan Tsarki A Mazahabar Ahlul-bait (AS).
Tun Farko Mutum Zai yi Niyya Ne Sai Ya Wanke Kansa Tare da Wuya, Amma Zai Ɗan Haɗa da Wani Ɓangare Na Ƙirjinsa Domin Samun Yaƙinin Shigar da Wuya Gaba Ɗaya.
Sai Mutum Ya Wanke Tsagin Jikinsa Na Dama Tun Daga Farkon Ƙirjinsa Har Ƙasan Tafin Ƙafarsa Shima Kuma Zai Ɗan Saka Wani Ɓangare Na Wuya Domin Samun Yaƙinin Shigar da Ƙirji Gaba Ɗayansa,
Kuma Za'a Ɗan Shigar da Wani Ɓangare Na Hagu A Cikin Wankin Domin Tabbatar da Ɓangaren Daman Ya Haɗe Gaba Ɗaya.
Sai Kuma A Wanke Ɓangaren Hagu Kamar Yanda Aka Yiwa Ɓangaren Dama.
Shikkenan An Gama Wanka A Sauƙaƙe Babu Wani Saɓani Ko Wani Ƙila Wa Ƙala Ko Su Wane Sun ce Kaza.
Yadda Kaga Wannan Wankan to Haka Ake Yin Kowanne Irin Wanka Kona Janaba Ko Haila Ko Wankan Mamaci Ko Wankan Juma'a da Sauransu illa iyaka Niyya Ce Take Banbanta Su.
Dole Ne A Jeranta Wankan Kamar Yadda Ka Gan shi A Jere, idan Mutum Bai Jera shi ba Kamar Yadda Yake, to Wankansa Baiyi ba.
Idan Mutum Yayi Wankan Janaba to Ba Sai Yayi Alwala ba Zai iya Yin Sallarsa Ko Kuma Ma duk Wani Aikin da Aka Sharɗanta Cewa Sai da Alwala Akeyin sa.
Amma Idan Mutum Yayi Wankan da Ruwan Kwace to Babu Wankansa.
Sannan Dole Ne Sai An Fara Kawar da Najasa Kafin A Wanke Kowacce Gaɓa Daga Cikin Gaɓoɓin Wanka Wato Ya Zama Gaɓar Tana Tsarkake Ne Kafin A Wanke ta.