Yadda Ake Yin Addu'ar Samun Mijin Aure

Yadda Ake Yin Addu'ar Samun Mijin Aure


Yadda Ake Yin Addu'ar Samun Mijin Aure


Girma ya fara kamani, shekaru na 28 amma har yau babu wani tsayayyen mutum da ya nuna yana sona da aure. Ina cikin damuwa, ga Mahaifana suma na ƙara tsufa cike da ƙunci, takaici, gami da damuwar rashin aure na. Allah subahanahu wata'ala ka yaye mana abinda ya dame mu.


Wato yana da kyau bayin Allah muke tuna cewa kowa na da irin jarabawar da Allah ke yi masa a rayuwa. Kada kurum don Allah ya jarabceka da abu kai tsaye idonka ya rufe ka tada hankali tare da kiɗima kanka. Ba haka sunnar rayuwa take ba.


Sai ma kana da imani ne Allah zai jarabceka, wani babu ruwan Allah dashi, kullum a saɓon Allah yake amma kuma na ƙara wadata shi da komi, wallahi wani ko jaki bai fishi lafiya ba amma kuma baya yiwa Allah komi da lafiyar sai saɓo. 


Jarabta gaskiya ce, dole ne mu yadda da wannan kafin ma mu iya bugar kirji cewa mu masu imani da Allah ne. Kar mutum ya makance ya zamto alkibla ɗaya kurum yake duba a rayuwarsa, wato abinda ya rasa, ba abinda yake dashi saɓanin saura ba. 


Kowa da Jarabawarsa

Wata akan jarabceta da Kansar nono (Breast cancer) yadda bama tsanani da wahalar ciwon ba A'ah kirjin baki ɗaya ya tafi an yanke nonuwan anzubar.

Wata ga Auren amma babu Haihuwa, Wata auren na dole nema da zata samu a sake ta yafi mata komi nan duniya. Wasu ga auren amma ƴaƴa duk kangararru sune ma sanadin mutuwar iyayen. 

Wasu kuma a jarabcesu ta hanyar rashin tsaro, ya zamto suna rayuwa cikin fargaba da tsoro, kisa da wulakanci koda kuwa suna da abinci da sha.

Wasu kuma tsanani daga shugabanni ya zamto suna azabtuwa daga salon mulkin su, shugabannin su yi ta sace arzikin kasa mutane na ƙara talaucewa

Wasu a jarabcesu da Faari na rashin abinci, ko ambaliyar ruwa tazo ta share komi.

Wasu kuma a jarabcesu da talauci, aikin ma da zakai ka sami abinci sam babu.

Wasu kuma a jarabcesu ta hanyar addininsu; Gasu musulmai amma suna rayuwa a ƙasar da basu da ikon fitowa su yi sallah, Matansu basu isa su sanya hijabi su fito waje ba, Mazaje basu da damar barin gemu don ɗabbaka sunnah, ana kama su ana rufewa a concentration camp, ƴan ƙasa ne amma sun rasa ikon addini, kurum don sunce basa bautar kowa sai Allah.

Muke tuna Allah ne ya halicce mu ne domin mu bauta masa kurum. Ba don mu yi gasa ba, kuma ɗaya daga cikin sharruɗan bautawa da biyayyar mu ga Allah shine mu zamto masu haƙuri da juriya acikin jarabawoyinsa. Allah na jarabtar mu ne don yaga waye zai iya cin jarabawar.


Ƴar uwa abinda ta bayyana shine; ke Jarabawar taki acikin Aure take, Har yanzu ubangiji bai turo Namijin da ya dace yazo ya nemi aurenki ba... DON HAKA MEYE ABIN YI kenan? 

Abinda zance shine; Shin kinyi imani da ƙaddara?

Idan kinyi imani da ƙaddara. Shin zama ya kamata kiyi kamar gunki kullum cikin tunani da dumbin damuwa Ko kuwa cirewa kanki hayaniya ki cigaba da Rayuwarki normal kamar kowa yadda Allah ya tsara miki kiyi?

Ki sani damuwa bata canza komi, idan har Allah ya tsara zaki aure tofa komi daren daɗewa ko kin shekara 50 sai kinyi. Idan kuwa Allah bai tsara bazaki ba bazafa ki yin ba koda kowa yazo yace yana sonki.

Tafiyarki cikin rayuwa zata ƙare ne da anfasa kukan kin Mutu. Don haka karki ɓatawa kanki lokaci ya zamto kin ɓata gobenki a ƙiyama wajen ƙorafi akan abinda baki da iko kansa,

Allah (SWT) ne kadai ya isa akan Hakan, Shine kuma zai tsara sanda ya yaga ya dace ki aure.

Tare da faɗin haka ɗin dai baiwar kullum ki zamo me kallon abinda Allah yai miki. Cikin komai akwai wani alkhairin da inba anyi aiki da hankali ba bakowa ke gane hakan ba.


Misali:

Kince baki da aure, shekarunki 28, iyayenki ma na cikin damuwa saboda rashin aurenki. Tom munji wannan.

Yanzu ki ɗauka cewa ga masoyi ya samu, wanda zuciyarki ta karɓa. Kunyi aure kuna zaune... Kwatsam sai ta soma bayyana Miji ne mai duka da cin mutunci, me gasa miki baƙaƙen maganganu da ganin cewa zama dake alfarma, bai damu da sallah ba, bai damu da addini ba, mashayin ƙwayoyi ne da sauran munanan ayyuka wanda duk abaya kafin ki aure sa baki san haka ba sai yanzu. 

Bayan zaman shekara 1 zuwa 3 wuya tai yawa kun rabu ya sallameki lokacin da yaro ko yarinya... Kin koma gidan iyayen nan dai naki, kin cigaba da rayuwa cikin ƙunci.

Shin wanne Yafi Alkhairi. Zamanki na kafin ki aure cikin nutsuwa da neman ilimi ko kuwa wannan zaman da zaki bayan faruwar waccan masifa? a irin wannan yanayin da mutum shi kadai ma da cikinsa ya ya iya ballantana. 

Don haka dole mu buɗe tunanin mu, komi Allah yai kwai hikima aciki. Ko yaushe ki zamo mai godiya ga Allah, ba mamaki da kinyi auren abinda zaki gani yafi wannan muni. Ki kokari ki shagala da wani abin, ki bar komi gun Allah. 

Bake kadai ba ga kowacce Mace dake cikin irin wannan yanayin ko yaushe a dage da addu'a kamar yadda aka saba, ake ƙoƙarin yin addu'ar kuma a lokutan da ake karɓar ta, wato:

1. A yayin sujjada "ya Allah ka azurta ni da Miji nagari, me addini, me arziki, mutunci da karamci. Allah ka karɓi wannan addu'ar tawa. 

2. Tsakanin lokacin da akai kiran sallah zuwa tayar da iƙama. Lokutta biyar a yini gasunan. 

3. Yayin saukar ruwan sama. 

4. Da kuma can karshe na kaso 1 bisa 3 na ƙarshen dare. 

Duk wannan lokutane da suka inganta da idan akai addu'a asu kai tsaye Allah ya karɓa. Insha Allahu duk sanda auren ya zamo shine alkhairi tofa zaki ga Allah ya turo miki miji ta inda bakya tsammani.

Sannan Mutane masu gwaɓawa mutane magana akan aure ku kuka da kanku, ku sani bada su kuke yi ba da Allah da ya halicce su kuke, shine kuke cin gyaran sa akan ba haka ya dace yai ba. Kuna cikin halaka.

Kuma da ya hore muku kusani ba wayonku bane. Shirme da hauka ne kaji mutum nama lissafin ai inkai auren wuri sanda zaka shekara kaza sannan danka ya kawo karfi zai ma kaza da kaza.

Guy's shin kai dama don abinda kai auren kenan don ka zamewa wani wahala ba don neman yardar Allah da samun ladan da ake samu a auren ba? Kayi ne don kake ciwa mutane fuska? waye ya baka tabbacin in mutum yai aure dolen dole zai haihu? Kafi Allah iya tsara abubuwa ne?

Ko kuwa wance kinƙi aure kaza da kaza duk kawayen ki sun yi kaza... Ina ruwanki? Toh ki aura Mata mijinki mana in kin damu da rayuwarta.

Bayin Allah ku yi hakuri da duk jarabawa, Babu wani lokaci da za'a ce ka makaro da aure, kurum yardar Allah ake nema. Wani gaggawar babu alkhairi ciki. Kwai wanda sukan yi suzo suna dana sani. 

Idan auren wuri ne guarantee na ƴaya zasu tallafawa mahaifa toh ka sani akwai wanda sun shekara 30 da aure ni kaina nasan su, kuma har yau basu haifi kowa ba.

Akwai kuma wanda yai auren wurin ya haihu amma ko yanzu da zai kwanta cewa bashi lafiya, babu ɗansa ɗaya da zai san ma bashi lafiya ballantana ya tallafa masa, don basa ta tasa.


Idan Anzo Batu Irin Wannan Na Kan Kalli Kaina Ko Yaushe 

Sanda Mahaifina ya haifeni ni Ibrahim Y. Yusuf ya wuce shekara 65 a duniya. Nine ɗansa na ƙarshe, kuma nazo masa a sanda bama ya kawo zai ƙara haihuwa toh amma Allah da ikonsa sai gani, ka dauka ace aure ne bai ba saida ya shekara 65, a hakan gashi akan idonsa Allah ya lamince saida na zamo Medical doktor, kuma kafin Sannan nai wasu karatuttukan daban. Don haka karka yadda wani banza ya dama maka lissafi.

Aure abin so ne amma inyai jinkiri a miƙawa Allah komi, kar ace ta kowacce hanya sai anyi. Karki taɓa yadda ki zina ko ki rasa ƙimarki don kina son mutum ya aureki. 

Malaman musulunci dukkan su sun tafi akan cewa yin Aure tabbataccen al'amari ne cikin shari'a. Sai dai Malaman kansu sun rabu uku dangane da hukunci akan Matsayin auren.

1. Rukunin farko sune wanda suke ganin wajibi ne kowanne mutum akalla yai aure sau 1 tak a rayuwarsa.

Ma'anar wajibi anan shine abinda idan kayi za'a baka lada, idan kuma baka yi ba ka aikata kuskuren da Allah zai iya maka azaba ko ya yafe maka. Masu irin wannan ra'ayin kwai irinsu Imam Hazmun, Imam Hambal, Imam Wa'ana da wasu daga cikin ɗaliban Imam shafi'i. 

2. Malamai na biyu; suka ce yin Aure Mustahabi ne. Wato abinda ba dole ne kan mutum ba. Anso kayi aure kuma idan kayi za'a baka lada, Amma idan bakayi ba baka da alhakin komi. Daga cikin irin wannan Malaman kwai Imam Malik, Imam Abu hanifa, Imam Shafi'i da Imam Ahmad tare da wasu cikin ɗaliban su.

3. Sai Malamai na Uku da suke ganin Matsayin aure ya rarrabu zuwa ga hukuncin AL-AHAKUMUT TAKALIFIYYAH wato hukunce-hukunce nan guda 5 na shari'a. A ganinsu aure ma ya karkasu zuwa gwargwadon masu yinsa. Sunce:

- Akwai wanda wajibi ne kuma tilas yai aure. 

- Wani haramun ne yai aure 

- Wani Anso yai aure, amma ba dole ne kanshi ba. 

- Wani kuma ba'a so yai aure ba sam (makaruhi). 

- Wani kuma da yin auren da barinsa duk ɗaya ne gunsa. 


Ga Misalin Su kamar Haka:

1. Wanda Aure yake Wajibi kansa. Shine; wanda yake da Lafiya, Sana'a, da kuma Lokaci, kuma sannan idan bai yi auren ba yana jin zai iya afkawa cikin baɗala da alfasha. Wannan tilas ne yai aure don kare mutuncinsa. 

2. Wanda Aure ya HARAMTA garesa kuwa shine; wanda baida lafiya, baida Sana'a, bai kuma da lokaci. Ko kuwa ya zamto baida ɗaya daga cikin abu ukun sama, kuma sannan bazai zina ba. Saboda idanma yai auren zai cuci matar, zai zalunceta, zaisa ta rasa hakkokinta na aure. Wannan idanma sunyi aure mutuwa zai. Don haka haramun ne. 

3. Wanda yake ANSO yai aure. Shine yana da lafiya, yana da Sana'a, yana d lokaci. Amma kuma ya shagala da wasu abubuwa na Ibadah. Toh wannan anso yai aure domin auren zai ƙara masa qima, da daraja, idan bai ba shikenan. 

4. Wanda yake MAKARUHI ne akansa, Wato ba'a so yai Aure ba. Wanda ya shagala da neman ilimi, ko rubuce-rubuce, ko karatu, yaɗa ilimi, ko kuma ya shagala da wani muhimmin al'amari wanda ya shafi addini, ko ya shafi al'umma, ko ya shafe shi a karan kansa shi. Kuma gashi baida sha'awa me karfin da zai yi zina, kuma idan yai auren wancan aure zai shagaltar dashi ga barin wancan abubuwan masu muhimmanci da ya toshewa al'umma ko musulmi kafar su. Don haka ba'a so yai aure ba wannan.

Shiyasa kwai wani littafi da wani marubuci ya kawo manyan malamai fitattu sama da 30 wanda basu taɓa yin aure saboda shagalarsu ga ayyukan ibadah da toshewa musulmi wata kafa wanda daga cikinsu akwai Imamu Nawawi, Imam Ibn taimiyyah, Imam ɗabari da sauran su. 

5. Sai wanda yinsa da barinsa duk daya ne. Wato idan yai auren zai ƙara masa kwazo, idan ma bai auren ba babu abinda hakan zai rage masa na himma. Sannan baida karfin sha'awar da zai baɗala ko alfasha. Shide kurum Neutral yake duk da ba'a cika samu ba, amma in ansamesa to da yinsa ko bari duk daya.

Wannan Kashe-kashen Haka Suke Har A Tsakanin Mata. Aita haƙuri tare da adduo'i. 


✍🏻

Ibrahim Y. Yusuf

Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post