Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki Da Sauran Wankan Tsarki

Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki Da Sauran Wankan Tsarki

Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki Da Sauran Wankan Tsarki 


Yadda Ake Wankan Janaba, Haila, Biki Da Sauran Wankan Tsarki 


Wankan Janaba yana da siffa guda biyu: Akwai 'siffatul ijza' (ta wadatar), da kuma wacce ake kira 'siffatu kamal' (ta kamala).


Wankan Janaba a siffar sa ta kamala shi ne: Idan kazo zaka yi ko za kiyi wanka ga ruwa a gabanka.


Farkon abin da zaka fara yi shi ne

Zaka karkato bakin mazubin ruwanka, ka wanke hannunka sau uku, sannan sai ka tsoma hannu a cikin ruwan sai ka debo ka wanke gaban ka, a dai-dai lokacin da zaka wanke gaban ka a lokacin zaka kulla niyya ta wankan janaba (Ko waninsa) wanda yake wajibi ne. 


Idan ka wanke gabanka ma'ana kayi tsarki kenan to daga nan kuma sai kayi alwala irin yadda kake alwala ta sallah, abin da duk kake a alwala ta sallah kayi, sai abu daya shi ne wanke kafafu to wannan zaka kyale shi ba zaka yi shiba, to daga nan sai ka tsoma hannunka guda biyu a cikin ruwan ba tare da ka debo ruwa ba sai ka murmurza kanka saboda kowane gashi da ya bude a lokacin da maniyyi yake kokarin fita daga jikinka ya koma yanda yake, don gashin dan Adam yakan bude musammam gashin sa na ka. 


Idan ka zuba ruwa a haka na iya haifar maka da ciwon kai ko wani abu daban, bayan haka sai ka debi ruwa a cikin tafin hannun ka daya sai ka zuba a kanka ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, ka sake kanfata na biyu ka tabbatar ya game ko'ina a kanka, haka na uku ka tabbatar ya game ko'ina a kanka.


To idan kayi wannan sai ka debi ruwa ka game dukkanin jikin ka da shi kana mai farawa da bangaren jikin ka na dama kafin na hagu, sannan na hagu ka tabbatar ruwa ya taba ko'ina.


To idan kayi wannan ne ka kammala, abu na karshe shi ne sai ka wanke kafar ka ta dama sannan kafarka ta hagu shine cikon alwalar da ka riga ka faro. Wannan ita ce siffa ta kamala a wankan janaba.


In wankan janaba ne haka zakayi, idan na haila ne haka za'ayi idanma wanka ne na biki haka mace zata yi, idan wankan jumu'a ne ma haka za'ayi, wankan idi ma haka zaka yi, banbanci kawai shi ne NIYYA.


Idan mutum zai yi siffa ta 'Al ijza' wadda ta wadatar ba sai kayi alawa a cikin ta ba, kana zuwa kayi niyyar yin wanka din kawai sai ka dauki ruwan ka watsa a jikin ka ya game ko'ina, idanma wani kududdufi ne ko rami ko swimming pool sai kayi tsalle ka fada a ciki, dama ka kulla niyyar ka kafin ka shiga, daga ka fito abin da zakayi shi ne abubuwa guda biyu, kurkurar baki da kuma shaka ruwa a hanci da facewa. Shike nan, kuma ya halatta kayi sallah da wannan wankan, Hadisi cikin Sahihu Muslim ya nuna haka.


Sai dai wanda ya yi wanka na farko ya fika kamala saboda ya bi dukkan sharuddan, ya fika cikar kamala, ya fika lada.


Kasancewar ba'ayi alwala ba ciki, wannan ka'idace ta malamai cewa karamin kari (HADATHUL ASGAR) idan sun hadu da babban kari (HADATHUL AKBAR) to da ka kawar da babban kari, karamin ma ya tafi. Amma ba lallai bane idan ka kawar da karamin ace babban ma ya tafi. Bissalam


Daga Marigayi Sheikh Jafar Mahmud Adam Kano.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

2 Comments

Previous Post Next Post