Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciya - Android Pols

Kannywood: Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciya
Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman Soyayya Masu Rasta Zuciya 


Kalaman Soyayya: Na karkato Cikin Zahirin Taskar Sabo Mai Kama da Yaduwar Sonki A cikin Birnin Fadar Masarautar Zuciyata


Dubun Amincin da Tsantsar Tsananin girman daraja Su Kara Tabbata akan Kyakkyawan Murmushinki Mai cikakkiyar Sura ta Alfarma, A Madadin Nisan Furucin Ayarin kalmomina, Ina Mai Isar da Sakon Sautin Amon Sassanyar Murya Zuwa ga Kunnuwan Sarauniyar da Duniya take Alfahari. 

Na karkato Cikin Zahirin Taskar Sabo Mai Kama da Yaduwar Sonki A cikin Birnin Fadar Masarautar Zuciyata, Hakika Kece Farar dabarar da Zan iya bayyanawa Kowacce Kalmar da ta Samo Asali Daga Sashen Bangaren dake Cikin Birnin Zuciyata.

Wannan Shine Makasudin Dalilin Yada Ambatonki Cikin Salon Kowace irin Murya, Dake na dauko Aniyar Fatan Mu Kasance Cikin Ayarin Tasirin Buwayar Kowane Harafi na Kalmar Soyayya, Fatana Shine kawar da Kowane Tunanin damuwa ko Makamancin haka Acikin Sararin Zuciyarki, Ni Zan Zamo Miki Garkuwa.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post