Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman So - Android Pols

Hafsat Idris: Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman So
Yadda Ake Tsara Budurwa Da Kalaman So 



Kalaman So: Domin suffarki sauyamin take tamkar wahainiya, hakanne yasa na kasa samun sunanki, matsayinki agareni bashida iyaka


Ya ke wacce tozali da kyakykywn murmushinta agareni yake zamowa silar kai sakon sanyaya ruhi gami da sanya daddadan nayi azuci da gangar jikina, shin ko kinsan kwangilar aikin da zuciyata ta baiwa kwakwalwata silar wallafuwar kaunarki a cikinta? Zuciyata tasa kwakwalwata na tinani akan kyakykywar suffarki, amma nagama tunanina kaf ban samo sunan da zan kira a matsayin naki ba. 


Domin suffarki sauyamin take tamkar wahainiya, hakanne yasa na kasa samun sunanki, matsayinki agareni bashida iyaka kinsan ko saboda me?  Sanadin soyayyarki shine silar wanzuwar kaunarki azuciyata daddar muryarki itace zumar da kunnuwa na ke son lasa, cikakkiyar kyakykywr surarki gami da ta kun ki daidai shine abu mafi dadin hange a idanuwana, kyakykywr kwalliyarki kuwa ita idanuna ke farauta a kowane lokacin. 


Zan kiraki da masoyiyata saboda kaunarki ce ma'abociyar rayiwar zuciyata, dalilin kiranki da abar kaunata kuma shine ruhina na samun salamane idan na tuna kewar kaunarki na zuciyata, da sunan kyakykyw zanyi maleji a duk lokacin da na tuna asalin kyakykywr fuskarki azahiri, mai daddadan sautin, zankiraki sanadiyar tunawa da dadadan kalamanki cikin sanyin murya agareni, tsawon lokacin da kika dauka kina mulkar zuciyata ne zai sa na kiraki da sauniyata.



Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post