Yadda Ake So Ango Ya Gyara Jikinsa Kafin Aurensa |
Yadda Ake So Ango Ya Gyara Jikinsa Kafin Aurensa Domin ya Gina jikinsa
Duba da Korafe-Korafen da suke Zuwar Mana Sakamakon Mutum yayi Aure Sai a wayi Gari Su Tsinci Kansu Cikin Babbar Matsala a daren Angwanci Wanda shine dare Mafi Mahimmanci a Wajen Ango da Amarya.
Amma wannan Daren yakan zama Dare mafi Muni ga Amarya da Ango, Ko a wayi Gari a wannan dare ya Zama mafi Shigar da Damuwa a zukatan Mutane biyu (Ango da Amarya) da suka dauki Watanni ko Shekaru suna Farantawa Junansu.
Tin daga Ranar da suka zama masoya guda biyu suna Kokarin Farantawa Junansu, tin daga wannan Ranar da suka Hadu a Matsayin Masoyan Juna. Sai a wayi Gari a Daren Angwanci sun Rasa Duk wannan Farin ciki da yake Lullube dasu a baya. Sakamakon Amarya ta sami Angonta ba yadda ta so ta same shi ba.
Ana Samun Wannan Matsalar, Sakamakon Rashin Samun Biyan Bukatar wannan Amaryar daga wajen Angonta.
Wallahi Yana iya Faruwa Ango ya shiga dakin Amarya Bayan Abokanansa sun Raka Shi, Idan sun tafi sun Barshi. Sai ya kasa yiwa Amarya komi, Zaiji Kamar Ma ba Namiji ba. Gabansa ya kasa ko Motsawa ko kuma ya wayi Gari Bashi da Wadataccen Ruwan Maniyyi Wanda hakan zai Iya kaishi ga Rashin Haihuwa ko kuma a wayi Gari ba zai Iya dadewa yana Iya Saduwa da Wannan Amaryar tasa ba. Minti biyar ko Goma ya Gama Ya Hakura. Wanda ba Mamaki Kuma Ita Daga Lokacin ne ma take Bukatar sa.
Amma Kuma Babu Labari Sai dai Barci Ita Kuwa zata kwana idonta Biyu a cikin Damuwa da Bacin Rai.
Wallahi Akwai wanda ya zo ya same Ni kamar zai yi Min Kuka Yana Gaya Min Matsalar da ya Fuskanta a daren Angwanci. Wai Amarya ma Fushi take yimasa. Anan ne na Zaunar da shi, na Bashi Kyakykawar Magana. Na Nuna masa cewar Daman ana iya Samun irin wannan Matsalar Na Nuna masa cewar ba fa ta kansa aka fara ba Anan Na Bashi Abubuwan da suka dace Tin daga wannan Ranar bai sake dawowa ba, Bayan Mun Hadu wani Lokaci Ya Nuna Min Cewar ae ga matsala ce ta Kawo shi Tinda babu wannan matsalar kuma shine bai dawo ba.
Yadda Ango Zai Yi Kafin Lokacin Aurensa
Saboda haka Shi Wanda aka sanya Masa Ranar Aure Yana da kyau Ya Tuntubi masani ilimin magani da zasu hadashi yayi tsaf, ya sha magani kamar yadda amare sukeyi tun saura wata 6 bikinsu ko wata 3, ka samu a hada maka Abubuwan da ake Bayarwa na Angwaye. Insha Allahu ba zaka Nemi Taimakon kowa ta wannan bangaren ba Sai dai Kawai ka Nemi Taimakon Allah.
Sai dai Kuma yana Faruwa wani ya Baka Maganin Bature Sabida Haka Kada ka Sake Wani ya Baka Magunguna irin na Bature. Sabida Illar da yake Haddasawa kamar Haka: Lalata Ido, Yawan ciwon Kai, Toshewar hanci, Kasala, Yoyon Fitsari, damuwa, fitsarin jini, Mantuwa da rudewa, qaiqayin maqogwaro, bushewar baki, kuma duk wanda ya dade yana amfani dashi gabansa zai daina aiki. Sannan Amfanin sa a Jikin Mutum na Iya Wannan Lokacin ne Kawai.
Shi Kuma Na Islamic Magani ne da yake Bin Jikin Mutum. Sabida Magani ne na itatuwa da kuma hade-haden Gargajiya Na Asali.
Abubuwan Da Ango Zai Fara Kafin Wata 3 Da Aurensa
1- ka samu habbatussauda, kustul Hindi, hulba, haltil, jinsen ka hadasu da dan yawa Ka nikasu sai ka dinga shansa kullum a shayi kamar teaspoon sau 3 a rana ko Kuma kadinga dafa cokali 2 a shayi kamar filas 1 kadinga Sha Kuma abin mahadin kada kasa suger sai dai mazar kwaila ko Zuma Mara hadi.
2- Zaka Fara amfani da Maganin sanyi Mai kyau da maganin basur kana Sha lokaci lokaci.
Cimakar Dake Sa Karfin Jima'i
Akwai wasu abinci da idan akayi anfani dasu suna sa kuzari ga da namiji misali Kamar su: Citta, barkono Ayaba, salak, Dabino, alaiyahu, albasa, wadanan ka mayar dasu sukan abinda kakeci idan kana Shirin aure da Bayan aurenka.
Cimakar Da Take Kara Karfin Maraina
Gyada, Garin gero, yayan itaciya, man zaitun, gayyanyaki, wake, Kara's, dankalin Hausa, yayan gurji da yayan kabewa da kwai na kazar gida da sauransu.
Cimakar Da Take Kara Ruwan Maniyyi
Ayaba, Tumatur, 'ya'yan kabewa, gyada da gyadar yarabawa, tafarnuwa, yin amfani da wadanan kafin aure da Kuma Bayan aurenka zai taimaka sosai.
Cimakar Da Take Da Jindadin Jima'i
Citta Mai kwaya, ayaba, gyada, Zuma, lemon Zaki, kubewa dabino busasshe, Aya, 'ya'yan kabewa da sauransu.
Abubuwan Da Ango Zai Bari Koma Yadaina Sha
Suger, lemon kwalba da na roba, Shan taba, shan giya, duk wani nau'in lemo da aka sawa suger ko kafi suger, dan zaki, sweetener duk sai ka barsu idan kanason ka Zama cikakken namiji.
Abubuwan Da Suke Sa Raunin Azzkari
Ciwon zuciya, hawan jini, yawan kitse a jiki, kunburin maraina, Rashin samun bacci, kankancewar maraina, ciwon suger, Shan suger, tunani da yawa da sauransu, wannan matsaloli da na lissafa idan kasan kana dasu ka Fara Neman magani kafin aurenka.
Daga Karshe, ya Kamata lalai maza su tashi tsaye wajen gyara jikinsu kafin aure domin wannan matslar tana da mutukar hadari ga rayuwar aurenmu a wannan zamanin domin Mata suna yin Sama da wata 6 suna gyara jikinsu da Shan magani kala-kala na sanyi da samun nishadi. Shiyasa Idan baka gyara ba kana kallon matar zata fi karfinka bazaka iya da ita ba sai dai kabarta cikin kunci da damuwa daga haka Kuma ta fara samin rauni da damuwa har ta Fara hango wani namijin bakai ba.