Yadda Ake Samun Kudi A Tiktok Cikin Sauki

Yadda Ake Samun Kudi A Tiktok Cikin Sauki
Yadda Ake Samun Kudi A Tiktok Cikin Sauki 


Hanyoyi 3 Na Yadda Ake Samun Kudi A Tiktok Cikin Sauki 


Shin wai dagaske ne ana samun kudi a Tiktok? Eh hakane ana samun dubban kudi har miliyoyi a manhajar Tiktok. Sai dai babban abin tambya da mutane ke yi musamman ma'abota shafin Tiktok shine taya ake samun kudin, ta wace hanya? Ku kalli wannan VIDEO 


Ga duk wanda yake da sha'awar samun kudi ta Tiktok to ya Karanta wannan rubutu har zuwa karshe ko kuma ku latsa wannan VIDEO domin jin cikakken bayani.


Akwai tabbatattun hanyoyi guda 3 da ake iya samun kudi dasu ta manhajar Tiktok, ga jerin hanyoyin kamar haka;


(1) Tiktok paid partnership; wannan wata hanya ce da manyan masu amfani da Tiktok ke samun kudi da ita, amma sai ka cika wasu sharudda kuma ka kai wani mataki na adadin mabiya(followers kafin ka Fara samun kudi dasu. Sannan Kuma sai ka tabbatar baka saɓa dokokin su ba.


(2) Branding Ko Marketing; wannan wata hanya ce da Zaka iya yiwa kamfani talla, su kuma kamfanin za su biyaka sakamakon wannan talla da ka yi musu. Sai dai babban abin tambaya anan shine, a ina Zaka samu wadannan kamfanoni da za kai musu talla har su biyaka? Kalli wannan video don ganin yadda zakai 


(3) Affiliate Marketing; Ita wannan hanyar ko yau ka fara Tiktok, ko bakada followers Zaka iya samun kudi dasu. Shi wannan sayar da kaya wani sannan ka samu kamasho daga kayan da ka sayar. Misali kamar link Zaka saka a shafinka duk wanda ya shiga tanan ya sayi kayan kai kuma za'a baka ladan yin hakan. Kuna iya kallan wannan VIDEO don jin Karin bayani. 


Wannan sune hanyoyi guda 3 nagartattu da ake iya samun kudi dasu ta manhajar Tiktok. Idan Kuna neman Karin bayani kun iya kallon wannan video don ganin yadda ake bin wadannan hanyoyi a saukake.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

1 Comments

Previous Post Next Post