Yadda Ake Samun Kai A Daren Farko Cikin Kabarin idan an mutu
Ɗan uwa, duk abinda zaka karanta ɗin nan babu tatsuniya ko ko kwanto a cikinsa. Zauren Fiqhu ya tattaro bayanin ne kan yadda ake tsintar kai a daren farko cikin kabari daga Sahihan Hadisai na Manzon Allah (S.A.W) waɗanda Manyan Malamai suka tattaro a cikin litattafansu.
Daren ka na farko a cikin ƙabarin ka shine dare mafi razani da firgitarwa daga cikin dukkan darare. Haƙiƙa tun lokacin da suka zo suka binneka, Idan sun ajiyeka a gefen ƙabarinka, Shi kansa kabarin zai yi magana dakai. Zai tambayeka shin Mai kake gani a cikinsa??
Zaka ce masa ai babu komai. Shi kuma zai ce maka, to duk abinda ka gani na alkhairi ko Sharri, to kaine kazo da abinka. Idan kai mutumin banza ne mai bin son zuciyarsa, mai biyewa Sha'awarsa, To shaiɗan ya riga yasan ya gama dakai.
Don haka zai zo gefen kabarinka yana yi maka dariyar Mugunta. Idan kuwa ka zamanto mutumin Kirki mai tsoron Allah, mai halayen Kirki, tun daga mutuwarka shaiɗan zai dinga tsula kuka da yin ihu wai saboda bai samu damar dulmiyar da kai cikin hallaka ba.
Yadda Mutum Yake Samun Kai A Daren Farko Cikin Kabari
Idan sun gama binneka, Allah zai dawo maka da ruhin ka cikin jikin ka. Nan take zaka riƙa jin maganganun ƴan uwanka amma babu damar ka amsa musu. Kana jin takun takalminsu amma babu damar ka tashi ka bisu. Idan kai Mumini ne cikakke, Nan take zaka ga wasu Mala'iku farare masu kyawawan kamanni za su shigo har cikin kabarinka. Za su yi maka sallama sannan su zaunar da kai su tambayeka :
"Wanene ubangijinka? Menene Addinin Ka? Kuma Mai Zaka Ce kan Annabi Muhammadu (SAW) - Zasu nuna maka siffarsa" Zaka basu cikakkiyar amsa: "Allah ne Ubangijina, Musulunci ne addinina. Kuma Annabi Muhammadu (SAW ) Shine Manzona nayi imani dashi. Shine ya isar min da sakon Ubangiji".
Nan take Mala'ikun za su yi maka kyawawan kalamai. Za'a nuna maka gidanka na Aljannah kuma za'a buɗe maka wata ƙofa wacce ta nan ne ni'imomin cikinta zasu riƙa shigo maka har zuwa ranar tashin Alqiyamah.
Idan kuma Kafiri ne ko Munafiki (Mai imani abaki, amma zuciyarsa babu Soyayyar Ma'aiki SAW) Ko kuma mai bin son zuciyarsa, awannan lokacin zai ga wasu Mala'iku baƙaƙe wuluk masu mummunar kamanni. Zasu shigo har cikin kabarinsa, su tasheshi su zaunar dashi Sannan su tambayeshi "WANENE UBANGIJINKA, MENENE ADDININKA, KUMA MAI ZAKA CE DANGANE DA ANNABI MUHAMMADU (SAWW)"
Zai ce "Aah! Aah! Ban sani ba! Ban sani ba!" Sai Mala'iku su fara Jibgarsa da wata irin gudumar Baƙin ƙarfe wacce ba zata misaltu ba. Idan ya kwarara ihu sai dukkan halittu sunji shi. in banda mutane da Aljanu.
'Wannan ranar tana nan zuwa garemu baki ɗaya. Dani da kai, da ke, da ku, duk Sai mutuwa ta riskemu. Kuma sai munyi kwanciyar kabari. Kuma sai an tambayemu akan ayyukanmu.
Shin sau nawa kake tuna wannan ranar a kullum?? Shin kana yin tanadi domin zuwanta?? Ko kuma tanadin gyaran duniyar ka kawai kakeyi?? Ni dai na duba cikin ayyukana ban ga wani abinda zan doshi Allah dashi ba. Sai dai imani, Son Allah da Manzonsa (SAW).
Ya Allah afuwarka nake kwaɗayi. Rahamarka nake roƙo, Falalarka nake saka rai. Ya Allah ka gafarta mana ka gafarta ma Iyayenmu da Malumanmu da iyalanmu da dukkan Musulmai maza da mata.
Waɗannan sune yadda mutum ke tsintar kansa a ranar farko cikin kabarinsa. Da fatan al'umma za ku nutsu kusan akwai ranar mutuwa kuma a koma ga Allah a yi ayyukan alheri.
Ka Tuna Da Daren Farko A Cikin kabarin ka