Yadda Ake Karya Sihiri Da Lalata Sharrin Aljanu |
Yadda Ake Karya Sihiri Da Lalata Sharrin Aljanu
ﺍﻋﻮﺫ ﺑﺎﻟﻠﻪ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﺍﻟﺮﺟﻴﻢ ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﺮﺣﻤﻦ
ﺍﻟﺮﺣﻴﻢ
Sihiri shine ne hadin kai tsakanin aljani da boka domin a cutar da wani mutum ta wata ɓoyayyiyar hanya.
A yanzu ina so ne in kawo muku yadda za ku lalata SIHIRIN da aka yi maka ko aka yi wa wani ko kuma korar Aljanun da suka damu mutane insha Allahu.
Amma yana da kyau in fara yin bayanin alamomin yadda in ka ji su a tare da kai za ka gane an yi maka sihiri ko kuma an yi wa wani, sannan in kawo maka yadda za ka warware shi ta hanyar Ayoyin Alqur'ani da addu'o'in Manzon Allah (SAW).
Yadda Zaka Gane Kana Da Aljanu Ko Kuma An Yi Maka Sihiri
Ana gane mai Aljanu ne ko wanda aka yi wa sihiri ta hanyoyi guda uku kamar haka:
1) Alamomin boye.
2) Alamomin sirri.
3) Alamomin zahiri.
Alamomin boye sune alamomin da shi mara lafiyar ne kawai ya ke iya ji ko ganin su a tare da shi Kamar haka;
- Yawan mafarki mai abin tsoro.
- Yawan ciwon kai dab da magriba.
- Jin abu na yi ma yawo a jiki kamar kiyashi.
- Haka kawai gaban mutum ya dinga faduwa.
- yawan mafarkin saduwa.
- Rashin son yin aure.
- Bacin rai mara dalili.
- Yawan tunane_tunane marasa amfani.
- Gane-ganen abubuwan tsoro kamar karnuka,
- macizai, kuraye da dai sauran su.
- Jin kasala lokacin da za ka yi sallah.
- Jin ciwon kai lokacin da ake karanta
- Alqur‘ani.
- Rashin fahimtar karatu ko kuma saurin
- zubewar sa, musamman ma na addini.
- yawan jin an kira sunan ka kuma ka waiwaya
- ba ka ga kowa ba.
- yawan jin kamar an caka ma ka kibiya ko
- allura a jiki.
- Za ka kwanta barci da wuri amma ya ki
- daukar ka sai dab da asuba.
- Yawan batan kudi ko kayan amfani.
- Yawan fada ko gaba da mutane da dai sauran alamomi.
Yadda Ake Gane Mutum Yanada Aljanu
Ya a ke gane mai Aljanu? ko wanda aka jefe
shi da Sihiri(kashi na biyu)
Ana gane mai Aljanu ne ta hanyoyi guda uku
kamar yadda mu ka fada tun a farko.
Za mu Dora da bayani