Yadda Ake Hira Da Mace Sabuwar Kamu

Yadda Ake Hira Da Mace Sabuwar Kamu
Yadda Ake Hira Da Mace Sabuwar Kamu


Matakan Yadda Ake Yin Hira Da Mace Sabuwar Kamu

 

Wani Yai Tambaya Kamar Haka;

Tsakani da Allah Ina son yarinyar nan amma ban san yadda zan fara tattaunawa da ita ba.  Da fatan za a taimaka.


Malam Tonga ina gaisuwa. Akwai wata da na fara soyayya da ita, wannan yarinyar ban san me zan rubuta ba. Kuma gashi ba na son rasa ta. Waɗanne irin hira da tambayoyi zan yi mata idan muna hira?


Malam ina son wata budurwa ce 'yar Jami'ar da nake karatu amma wallahi na rasa yadda zan tinkare ta da zancen soyayya. Don Allah a taimaka.

 

Waɗannan wasu saƙonni ne da nake samu daga wajen samarin da suke son sanin irin hiran da za su riƙa yiwa 'yan matan su sabbin kamu. Wasu kuma suna son sanin dabarun da za su tinkari macen da suke so a karon farko.


Mun sha yin darussa a kan dabarun tinkaran mace. Sai dai irin hiran da namiji ya kamata yayi da sabuwar kamunsa shine ba mu yi su da yawa ba. Wannan yasa zamu yi bayani ne akan sa.

 

Ba wai kawai samun soyayyar mace shine abun bukata ba. Rashin sanin yadda za ka yi hira da mace na iya sa ka rasa wannan budurwa da ta amince da soyayar ka.


A ɗabi'a ta mace, tana son namiji shuru-shuru. Amma bata son namiji mara magana. Shi shuru-shuru saboda son kanta na kada ya saba da wasu matan da kuma zai yi sauƙin kai da kowace mace ma zata nemi yin kusanci da shi. 


Wannan yasa mata suke son maza masu shuru-shuru. Amma sam bata kuma son saurayinta ko mijinta ya kasance mutumin da bai magana sam, ko bai iya hira ba. Saboda mace duk yawan maganarta da surutun ta tana son taji wanda take so shima yana cewa.

 

Wannan rashin iya hira da mata yasa samari ko nace maza da dama suna ji suna gani suke rasa soyayyar su wajen matan da suke so.


Sai dai abu na farko da namiji zai fara yin duba dashi shine, hira ya zame masa dole koda kuwa ba dabi'ar sa bane domin tabbatar da ya samu abinda yake nema. Don haka dole ne ya daure ya koyi sakin baki a gaban wacce yake so domin gudun kada wani mai iya zance yayi wuf da ita.


Zance da mace musamman sabuwar kamu yana da matakai, saboda a wannan lokacin baku gama sanin juna a soyayya ba koda kuwa a gida guda kuka taso. Don haka akwai maganganu ko tambayoyin da ba zaka yi mata ba a farko-farkon fara soyayyar ku. 


Mu ɗauka ka riga da ka samu soyayyar ta za ka soma zuwa wajenta hira, taɗi ko zance. Akawai wasu matakan hira guda 7 da su ya kamata duk wani sabon masoyi ya yiwa sabuwar kamunsa. 


Waɗannan matakan kuwa sune kamar haka:

1: Tamboyin neman saninta da kyau: Wannan shine hiran da duk wani sabon saurayi zai fara yiwa sabuwar kamunsa a soyayya. A wannan lokacin akwai wasu abubuwan da zaka so sani game da ita masu mahimmanci. Kafin ka bata dama ita ma ta yi maka nata tambayoyin.


A wannan lokacin kai aikinka sauraro ne wajen bata hankalinka, da kuma yi mata ƙarin tambaya akan bayanin da baka gane ba ko baka fahimce ta ba. A wannan yanayin itace zata zama mai maganar ba kai ba. Amma domin hira ya mata dadi, kuma taji cewa hira take da masoyinta a soyayya, dole ne ka tabbatar baka amsa wayarka ba ko wasa da wayar taka.


Haka kuma ya dace ka riƙa binta da tabbatar mata kana sauraronta yadda ya dace da kuma fahimtar ta ta hanyar amsa mata da kuma kaɗa kanka a matsayin kana gamsuwa da jawabin nata. A wannan lokacin ka tabbatar da cewa idanuwanka yana kan fuskanta kana yi mata kallon soyayya da ƙauna. 


Kada ka maida hankalinka wajen kallon ƙirjinta idan mai yalwar ƙirji ce. Hakan zai sa ta yi maka fassara na daban. Amma kallon fuskanta da ƙwayar idanuwanta aikawa ne da saƙon soyayar ka gareta. Rashin ƙura mata idanuwa kuma zai nuna tamkar bata yi maka bane. Don haka ajiye kunya zaka yi a gefe kayi abunda ya dace.


A wannan lokacin da take magana idan baka fahimci wani waje ba ko bakaji sosai ba, yi mata magana cikin wayewa na baka fahimce ta ba. Kada ka barta tayi ta zuba kamar tana hira da ɗan jarida ne ba tare da kana katsaita kana yi mata wasu tambayoyin ba. Hakan yana nuna mata kana tare da ita kuma kana gamsuwa da amsar da take baka.


Kafin ka san irin tambayoyin da suka dace da zaka yiwa sabuwar kamunka, yana da kyau ka fahimci cewa, shi sabon masoyi a soyayya duk yadda yake son hira da sabuwar kamunsa ba a so ya jima. Don haka kada ka sake idan kaje sai an turo ta shiga gida ko kuma lokacin shiganta gida yayi kana tare da ita.


Dogon lokaci kana hira da ita zai jawo kayi ta maimaita batu iri guda, ko ka rasa ma abun cewa idan ba haɗawa zaka yi da karya ba kuma abunda ba a so kenan. Hakan nan jimawa da ita ba zai baka damar ta zama tana ɗokinka ba. Zaka yi ta zuba ne ko ka yi ta saka ta surutu har sai ta gaji da kai. Don haka ne ba a son jimawan a lokacin da kuke tsakiya da hira za ka yi sallama da ita.


Haka nan taƙaita doguwar hira wajen sabuwar kamunka nasa iyayenta idan masu hankali ne su fahimci kanada tsari kana da abunyi ba mara aikinyi bane koda kuwa shidin ne.


Rashin barin har sai mace tace maka zata shiga gida ka sallami kanka yana cusawa mace shakku a ranta da zata riƙa jin abun na damunta a rai. 


Zata rika tunanin ko dai itace bata yin abinda zai saka jimawa a wajenta, ko kuma kana barinta kaje wajen wata budurwa. Wannan shakkun ribace a soyayyar ka.


A darasi na gaba zamu kawo irin tambayoyin da suka dace ka yiwa mace sabuwar kamunka a sabon soyayyar ka da ita.


Suleiman Inuwa

I am a professional website developer and also an SEO expert.

Post a Comment

Previous Post Next Post