Yadda Ake Haɗa Shayin Goriba Da Amfani Da Yake Yi Ga Jiki |
Amfanin Shayin goruba da ayyukan da yake yi a jikin mutum ba za'a iya bayyana su ba
Ka Nemi Aya Amma busassa Mai kyau daidai buƙata, sai ka Nemo garin goriba wacce aka daka sai ka haɗe waje ɗaya ka niƙa har su zama gari, sannan sai ka tankaɗe. Ka nemi ruwan ɗumi daidai girman kofi, sai ka sanya cokali uku manya a ciki idan ya huce sai ka Sha.
Zaka Sha da safe da Kuma lokacin kwanciya bacci. Maganine Mai ƙarfi Mai ɗanɗano Mai amfani ga ilahirin gangar jiki da ruhi. Ga kaɗan daga cikin magungunan da wannan shayin na goruba yake yi kamar haka;
- Yana buɗa ƙwaƙwalwa.
- Yana narka abinci nan take idan aka sha bayan an ci abinci.
- Yana karawa namiji ƙarfin azzakari.
- Yana ƙarawa namiji yawan ruwan maniyi
- Yana Ƙara lafiyar jima'i da sha'awa ga ma'aurata, sai a riƙa sha akai-akai.
- Yana Kara ƙarfi da cire kasala a ji garau a jiki.
- Yana ƙarawa macce ruwan ɗumi na ni'ima
- Yana ƙarawa zuciya lafiya da ƙarfin aiki.
- Yana wanke hanjin ciki da suka cushe saboda ciye ciye ba maiƙo da zaƙi.
- Yana Maganin kumburin ciki da tsutsar ciki da zafin ciki da kullewar ciki.
- Yana samar da ƙwayoyin halittan haihuwa na Mata da maza.(sperm and ovum)
- Yana maganin rama a jiki
- Yana ƙara yawan immunity da ƙarfin aiki.
- Yana yaƙar cutukan daji da na cancer
- Yana maganin ƙurajen ciki dana cikin Baki natural vitamin C ne Mai ƙarfi.
Waɗannan kaɗan ne daga cikin magungunan da shayin goruba yake yi ga jikin dan adam idan ana amfani dasu. Kuma ba wai iya maza ne kaɗai za su dinga sha ba har da mata suma yana yi musu aiki sosai. Da fatan za ku dage wajen yin amfani da shayin goruba akai-akai.